Musayar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Sane, Moses, Jorginho, Werner, Ighalo, Lemar

Leroy Sane

Asalin hoton, Getty Images

An ajiye wa danwasanManchester City da Jamus Leroy Sane, dan shekara 24, rigar wasa mai lamba 10 a Bayern Munich idan ya koma kungiyar a kakar wasa ma zuwa, a cewar jaridar (Mirror).

Chelsea tana fama a yunkurinta na sayar da Victor Moses a yayin da Inter Milan ta ki amincewa ta biya £10.75m a kan dan wasan na Najeriya mai shekara 29, in ji (Sun)

Wakilin Jorginho ya dage cewa dan wasan na Italiya yana cike da farin ciki a zaman da yake yi a Chelsea yana mai yin ikirarin cewa Juventus bata tuntubi dan wasan dan sekara 28 ba. (Metro)

Ana rade radin cewa Sevilla za ta kashe euro 20m domin sayo golanTrabzonspor wanda Leicester City take son daukowa Ugurcan Cakir, mai shekara 24. (Leicestershire Live)

Liverpool ta shirya tsaf domin sayar da 'yan wasa uku a bazara domin ta samu £52m wajen sayo dan wasan RB Leipzig da Jamus Timo Werner, mai shekara 24. (Athletic - subscription required)

Manchester United tana son Odion Ighalo, wanda ta karbo aro daga Shanghai Shenhua, ya ci gaba da zama a kungiyar amma hankalinta ya "kwanta" game da makomar dan wasan na Najeriya bayan Marcus Rashford ya dawo kan ganiyarsa. (Sky Sports)

Arsenal tana duba yiwuwar yin musaya inda dan wasan Atletico Madrid dan shekara 28 Alexandre Lacazette zai koma Spaniya, yayin da Thomas Lemar, mai shekara 24, zai koma Old Trafford. (AS - in Spanish)

Neymar, mai shekara 28, ba zai bar Paris St-Germain domin sake komawa Barcelona a bazara ba saboda tasirin da annobar korona ta yi kan hanyoyin samun kudin kungiyoyin kwallon kafa, a cewar wakilin dan wasan na Brazil. (Star)

Zagayen farko na Gasar Kofin Carabao yana fuskantar matsala idan ba a soma kakar wasa kafin watan Satumba ba. (Telegraph - subscription required)