Willy Caballero: Zai ci gaba da tsare ragar Chelsea kaka daya

Chelsea goalkeeper Willy Caballero

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Caballero ya koma Chelsea a 2017 daga Manchester City

Mai tsaron ragar Chelsea, Willy Caballero zai ci gaba da tsaron ragar kungiyar zuwa karshen kakar badi.

Tun farko an yi tsammanin golan mai shekara 38 dan kasar Argentina zai bar Stamford Bridge da zarar kwantiraginsa ya kare a watan Yuni.

Caballero ya kama gola sau tara a bana kafin a dakatar da wasanni cikin watan Maris, saboda tsoron yada cutar korona.

Biyar daga cikin fafatawar ya yi sune a cikin watan Fabrairu, bayan da koci Frank Lampard ya ajiye Kepa Arrizabalaga a benci.

Caballero fitatce ne a kungiyar Chelsea ya kuma bi sahun Olivier Giroud wanda ya tsawaita kwantiraginsa a Stamford Bridge zuwa wata 12 masu zuwa.

Kawo yanzu ba a san makomar Willian da Pedro ba, wadanda yarjejeniyarsu da Chelsea zai kare a karshen watan Yuni.

Caballero mai shekara 38, ya koma Stamford Bridge daga Manchester City a 2017.