Lampard na son a tsawaita zaman Willian da Giroud a Chelsea

Willian and Giroud

Asalin hoton, Getty Images

Frank Lampard na fatan Chelsea za ta tsawaita yarjejeniyar 'yan wasan da kwantiraginsu zai kare a Yunin nan, domin su karasa buga Premier bana.

Willian da Olivier Giroud suna daga 'yan kwallon da yarjejeniyarsu zai kare a Stamford Bridge ranar 30 ga watan Yunin shekarar nan.

Sai dai dokar da aka kafa bayan bullar cutar korona ta amince 'yan wasa idan sun yadda su buga wasannin da suka rage a Premier.

A makon da za mu shiga ake sa ran kungiyoyin Premier za su ci gaba da tattaunawa don zakulo hanyoyin da ya kamata a karkare kakar tamaula ta 2019-20.

Ana sa ran 'yan wasan Chelsea za su koma atisaye a tsakiyar mako, inda za su fara a matakin na daidai ku kafin daga baya su koma yi a matakin kungiya.

Lampard ya ce da zarar an koma ci gaba da gasar Premier bana 'yan kwallo da dama za su gaji, ganin za a yi wasanni da yawa, saboda haka suna da bukatar zama tare da wadanda suke da su.

Cikin watan Maris aka dakatar da gasar Premier, inda Liverpool ke mataki na daya a kan teburi da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City ta biyu.

Chelsea tana mataki na hudu a kan teburi, bayan buga wasa 29 da makinta 48, tana kuma buga gasar Champions League ta bana.