An tsayar da ranar sauraren karar hana Chelsea sayen 'yan kwallo

Chelsea FC

Asalin hoton, Getty Images

A watan gobe ne za a fara sauraren daukaka kara da hukumar kwallon kafar Ingila ta yi kan hana Chelsea sayen 'yan wasa.

Hukumar ta daukaka kara ne a kotun sauraren kararraki ta duniya, bayan da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta hukunta Chelsea.

Tun baya FA ta ce za ta daukaka kara bisa tara da aka yi mata kan hukuncin hana Chelsea sayen matasan 'yan wasa, bayan da aka sameta da karya ka'ida.

Kotun kararrakin wasanni ta duniya wato CAS ta tsayar da ranar 26 ga watan Yuni domin sauraren karar.

A cikin watan Fabrairun 2019 aka hana Chelsea sayen 'yan kwallo zuwa kaka biyu ta tamaula, kodayake daga baya an rage hukuncin inda aka amince ta dauki 'yan wasa a watan Janairu.

A lokacin da aka hukunta Chelsea an kuma ci tarar FA fam 391,000 daga baya aka rage zuwa fam 350,000.

An kuma bai wa hukumar kwallon wata shida domin ta shawo kan matsalar sayo 'yan wasa matasa daga wasu kasashen.

Tun a lokacin FA ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin za kuma ta ci gaba da tuntubar Chelsea da hukumar kwallon kafa ta duniya domin kamo bakin zare.