Chelsea ta daukaka kara ga FIFA

Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta daukaka kara ga hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA kan dakatar da ita da yi daga sayen matasan 'yan kwallo kafa.

A makon jiya ne hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta dakatar da Chelsea daga sayen sabbin 'yan wasa, saboda karya dokokin daukar matasan 'yan wasa da kulob din ya yi.

Hukumar ta ce an karya doka a kan sayen 'yan wasa 29 daga cikin 92 da kungiyar ta dauka.

Haramcin wanda zai kai har zuwa karshen watan Janairun 2020, ba zai hana Chelsea sayar da nata 'yan wasan ba.

Kuma ba zai shafi kungiyar mata ta kulob din da kuma ta kwallon kafar Futsal ba, wato masu taka leda a rufaffen daki.

Haka kuma Fifa, ta ci tarar kungiyar fam 460,000, inda ita kuma hukumar kwallon kafar Ingila ta FA aka ci ta tarar fam £390,000.

Haramcin ya zo ne bayan wani bincike da Fifa ta yi a kan wasu matasan 'yan kwallo da Chelsea ta saya, har da tsohon dan wasan gabanta Bertrand Traore.