Sane ba ya son komawa Liverpool, Manchester United tana zawarcin Traore

Manchester City's Leroy Sane

Asalin hoton, PA Media

Dan wasan gaba na Manchester City Leroy Sane ba ya sha'awar komawa Liverpool. Dan wasan mai shekara 24 dan kasar Jamus yana kan bakansa na son komawa Bayern Munich.(Bild, via Sports Illustrated)

Dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland, dan shekara 19, ya ki amsa tayin komawa Juventus a Janairu saboda kungiyar ta Italiya ta yi shirin saka shi a tawagar 'yan wasan da ke buga gasar 'yan kasa da shekara 23. (La Repubblica, via Star)

Manchester United tana cikin kungiyoyin da suka fi samun damar dauko dan wasan Wolverhampton Wanderers Adama Traore, inda ta bi sahun Liverpool da Manchester City wajen zawarcin dan wasan na Spaniya mai shekara 22. (Birmingham Mail)

Arsenal tana fatan dauko dan wasan Bayer Leverkusen dan kasar Faransa mai buga gasar 'yan kasa da shekara 21 Moussa Diaby. Tsohon dan wasan na Paris St-Germain mai shekara 20 ya taimaka sau biyu wajen ganin Leverkusen ta yi galaba a kan Werder Bremen a gasar Bundesliga ranar Litinin. (Le10Sport - in French)

Chelsea tana kan gaba wajen yunkurin dauko dan kasar Netherlands Mbuyamba dagaBarcelona, a cewar wakilin dan wasan dan shekara 18. (Voetbal International, via Mail)

Dan wasan Ingila da ke zaman aro aNewcastle United Danny Rose, mai shekara 29, ya yi amannar cewa Mauricio Pochettino - tsohon kocinsa a Tottenham Hotspur - zai jagoranci Manchester United"wata rana".(The Lockdown Tactics, via TeamTalk)

Kungiyoyin kwallon kafar Turai da dama suna son dauko dan wasan Tottenham Jan Vertonghen, wanda kwangilarsa za ta kare a bazara. Real Betisda Valencia sun yi tayin bai wa dan wasan na Belgium mai shekara 33 kwangila, sannan kuma kungiyoyin Italiya Inter Milan da Roma suna duba yiwuwar zawarcinsa. (Star)

Za a kyale dan wasan tsakiya naManchester United James Garner, dan shekara 19, ya bar kungiyar don zuwa zaman aro a kakar wasa mai zuwa, inda aka ce Cardiff City, Swansea City da kuma Sheffield Wednesday suna sha'awar dauko dan wasan. (Mail)