Cristiano Ronaldo ya fara atisaye a Juventus a karon farko

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Cristiano Ronaldo ya fara atisaye a Juventus ranar Talata, bayan kwana 72 rabonsa da kungiyar har da mako biyu da ya yi na killace kansa.

An dauki hoton dan wasan mai shekara 35 a lokacin da ya isa sansanin horon Juventus a wata bakar mota, daga nan ya je aka gwada lafiyarsa, sannan ya shiga cikin 'yan wasa suka motsa jiki.

Ronaldo ya koma Madeira a Portugal, bayan karawar da Juventus ta doke Inter Milan 2-0 a wasan da suka yi ba 'yan kallo ranar 8 ga watan Maris, daga nan ne aka dakatar da wasanni saboda bullar cutar korona.

A farkon watan nan ya koma Italiya a cikin jirgin samansa, amma sai da ya killace kansa mako biyu kamar yadda gwamnatin Italiya ta bukata don gudun yada cutar korona.

Ranar 4 ga watan Mayu kungiyoyin da ke buga Serie A suka koma atisaye a cikin rukuni dauke da mutune kadan da kuma bayar da tazara kamar yadda gwamnati ta umarta.

Gwamnatin Italiya na kan tattaunawa kan ko ya kamata a ci gaba da gasar Serie A, sai dai a ranar Litinin ta ce za a ci gaba da zama yadda ake yanzu har sai 14 ga watan Yuni, kwana daya tsakanin da ake fatan ci gaba da kakar 2019-20.

Gonzalo Higuain bai samu halartar atisayen ba, bayan da ya isa Italiya ranar Alhamis sai kuma ya yi kwana 10 a killace kan ya fara fita.