Karon farko Ronaldo ya ci kwallo uku rigis a Serie A

Asalin hoton, Getty Images
A karon farko Cristiano Ronaldo ya ci kwallo uku rigis a gasar Serie A, bayan da Juventus ta doke Sampdoria 4-0 ranar Litinin.
Ronaldo ya fara cin kwallo a wasan, bayan da Ragnar Klavan ya yi kuskure a farkon komawa zagaye na biyu a karawar.
Haka kuma shi ne ya ci na biyu a bugun fenariti, sannan ya bai wa Gonzalo Higuain kwallon da ya ci na uku.
Sannan ya ci na hudu na kuma uku a wasan, sannan karo na 56 a tarihi da yake cin kwallaye uku rigis a wasan tamaula.
Mai shekara 34 ya ci kwallo a kowanne wasa biyar da ya buga a Serie A ta bana, wanda ya koma Juventus a 2018 kan kan miliyan 99.2.
Wannan ne karo na biyu da Ronaldo ya ci wa Juventus kwallo uku rigis, bayan bajintar da ya yi a Champions League a karawa da Atletico Madrid wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.
Tun daga lokacin ya kuma zura kwallo uku rigis sau uku a tawagar kwallon kafar Portugal.
Tsohon dan wasan Manchester United, shi ne na farko tun bayan Alexis Sanchez da ya ci kwallo uku rigis a Premier da La Liga da kuma Serie A.











