Za a hukunta Walker saboda karya dokar hana fita

Kyale Walker

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Manchester City, Kyle Walker zai fuskanci hukunci, bayan da ya karya dokar hana fita inda ya shirya wani bikin da ya gayyato karuwai.

Walker ya nemi afuwa ya kuma yi kira da kowa ya zauna a gida a lokacin da ake daukar matakan hana yada coronavirus.

A wani bayani da City ta fitar ta ce ''dabi'ar da dan wasan tawagar Ingila ya nuna ta ci karo da halayyar da ya kamata ya gwada a matsayinsa na abin koyi ga na baya.''

Ta kuma kara da cewar za ta gudanar da bincike kan dan wasan domin fayyace abinda ya faru a lokacin da aka bukaci kowa ya killace kansa.

Gwamnati ce ta bukaci mutane su bayar da tazara a lokacin yin mu'amala su kuma zauna a gida a kokarin dakile yada coronavirus.