Ya kamata a bai wa Liverpool kofin Premier — Gundogan

Asalin hoton, PA Media
Adalci ne idan aka bai wa Liverpool kofin Premier na bana, idan har ba a kammala wasannin shekarar nan ba saboda coronavirus.
Wannan batun ya fito ne daga bakin dan kwallon Manchester City Ilkay Gundogan.
An dai kakatar da gasar Premier ta Ingila, wadda ake sa ran ci gaba da fafatawa ranar 30 ga watan Afirilun 2020.
Liverpool wadda rabon ta da kofin Premier tun bayan shekara 30, tana ta daya a kan teburin bana da tazarar maki 25 tsakaninta da ta biyu Manchester City.
Ranar 3 ga watan Afirilu ne kungiyoyin Premier za su tattauna ko za a sake daga gasar bana a lokacin ko kuma da damar ci gaba da ita idan coronavirus ta yi sauki.
A karshen mako ne shugaban hukumar kwallon kafar Turai, Uefa, Aleksander Ceferin ya ce sai dai a soke kakar shekarar nan idan har ba a ci gaba da wasanni a karshen watan Yuni ba.







