Ana buga gasar tamaula a Belarus duk da coronavirus

Belarus FA

Asalin hoton, Getty Images

An dakatar da dukkan wasannin kwallon kafa a Turai da wasu sassan duniya saboda coronavirus, amma ana ci gaba da wasanni a kasar Belarus.

A baya can ba kasafai ake maganar gasar kwallon kafar Belarus ba, amma yanzu tana bakin mutane ganin ita ce tilo a Turai da ke ci gaba da gudanar da harkokin tamaula.

A ranar Asabar an buga manyan wasanni shida a kasar har da wasan hamayya tsakanin FC Minsk da Dinamo Minsk, wanda mutum 3,000 suka kalli karawar a babban birnin kasar.

Kasa da mutum 100 ne suka kamu da coronavirus a kasar, wadda babu wanda ya mutu a kasar mai mutum miliyan 9.5.

Yayin da kusan baki dayan Turai suka killace kansu da rufe iyakokinsu, shi kuwa shugaban Belerus, Alexander Lukashenko bai damu ba, inda ya yi kira da 'yan kasa su sha barasa "vodka" don yakar coronavirus.

Sai dai shugaban hukumar kwallon kafar Belerus, Aleksandr Aleinik ya ce sun dauki matakan da suka dace kan dakile yaduwar coronavirus shi ya sa suka ci gaba da wasannin tamaula.