Coronavirus: Dan Chelsea Hudson-Odoi ya 'warke'

Callum Hudson-Odoi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Callum Hudson-Odoi ya buga Chelsea wasanni 13 a kakar wasa ta bana

Dan kwallon Chelsea, Callum Hudson-Odoi ya 'warke' daga cutar coronavirus, in ji kocinsa Frank Lampard.

Dan Ingilan mai shekaru 19, ya kasance dan kwallon premier na farko da ya kamu da cutar Covid 19 a farkon wannan watan.

"Na yi Magana da shi tun a makon farko da ya soma ciwo, abin babu dadi," in ji Lampard.

"Muna murna bai sha wahala ba, kuma a yanzu ya warke."

Chelsea ce ta hudu a kan tebur lokacin da aka dakatar da gasar Premier a ranar 13 ga watan Maris.