Coronavirus: Dan wasan Chelsea Hudson-Odoi da kocin Arsenal Mikel Arteta sun kamu

Callum Hudson-Odoi

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan gaba na Chelsea Callum Hudson-Odoi ya zamo mutum na farko a Gasar Premier ta Ingila da ya kamu da cutar coronavirus.

Haka ma kocin Arsenal Mikel Arteta ya killace kansa bayan da aka gano yana dauke da cutar.

An daga wasan da Arsenal za ta buga da Brighton a ranar Lahadi amma har yanzu ba a dauki mataki kan wasan Aston Villa da Chelsea da za a yi a wannan ranar ba.

Hukumar Gasar Premier za ta yi taron gaggawa a ranar Juma'a don tattauna makomar wasannin da za a buga nan gaba.

Sahsen Wasanni na BBC ya fahimci cewa wani mataki da mai yiwuwa a dauka shi ne na dakatar da wasanni tsawon mako biyu har sai lokacin da aka sanya na dan gajeren hutun da dama ake bayarwa nan gaba a watan nan, sai dai da wuya a dakatar da wasannin wannan kakar gaba daya a yanzu.

Dukkan kungiyoyin za su amince da yarjejeniyar duk wani mataki da aka dauka sannan za a sanar da jami'an gwamnati duk halin da ake ciki.

Taron manyan jami'an EFL da za a yi ranar Juma'a zai dauki mataki ne kan wasannin karshen makon nan da na gaba, kuma da alama za su bi matakin da Premier za ta dauka.

A ranar Juma'a Everton ta sanar da cewa dukkan 'yan wasa 11 na farko da kuma koci da mataimakansa sun killace kansu bayan da wani dan wasan ya nuna alamun cutar.

Chelsea ta ce Hudson-Odoi "ya nuna alamun cutar maibkamar 'yar mura da safiyar Litinin'' sai ya bar filin atisayen.

Kungiyar ta kara da cewa dan wasan ''yana samun sauki kuma zai koma bakin aikinsa da zarar ya ji sauki.''

A ranar Juma'a, dan wasan mai shekara 19 ya wallafa a Twitter cewa: ''Kamar yadda watakila kuka sani na kamu da coornavirus a kwanakin da suka gabata.

''Ina bin matakan lafiya da kuma killace kaina daga kowa na tsawon mako guda. Ina fatan gainin kowa nan kurkusa da fatan komawa bakin aikina.''

Shawarwarin da Hukumar Lafiya Ta Ingila ta bayar sun ce mai yiwuwa mutane da dama ba za su kamu da cutar daga mai dauke da ita ba idan har ta kwana bakwai a jikin mai cutar.

Sannan an shawarci mutane da suka yi wata mu'amaka da mai dauke da cutar amma ba su nuna alamu ba da su killace kansu tsawon kwana 14.