PSG ta bayar da Yuro 100,000 don yakar coronavirus

PSG

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar Paris St-Germain ta bayar da gudunmuwar Yuro 100,000 don a yaki coronavirus a Faransa.

Kudin zai taimaka wajen agaza wa kananan yara da tsofaffi da wadanda basu da muhalli da suka kamu da cutar.

Haka kuma za a yi amfani da kudin wajern taimakon likitocin da ke aiki don dakile cutar da yi wa 'yan sa kai bita kan kula da marasa lafiya.

Kasar Faransa ce ta biyar a duniya da aka samu wadanda suka mutu da yawa, sakamakon cutar, inda sama da mutum 1,300 suka mutu.

Shugaban Secours Populaire cibiyar da ke tallafawa gajiyayyu a Fransa, Thierry Robert ya ce sama da jami'ai 80,000 da 'yan sa kai na murna da wannan agajin daga Paris St Germain.

Ya kara da cewar wannan gudunmuwar za ta rage radadi daga wadanda suka kamu da coronavirus.