Guardiola ya bayar da kudi don yakar coronavirus

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya bayar da gudunmuwar Yuro miliyan daya domin yakar coronavirus da ta barke a Spaniya.
Guardiola, wanda ke hutu a gidansa da ke Barcelona, yana aiki tare da lauyoyinsa a kwanakin nan kan yadda zai taimaka da dukiyarsa.
Spaniya tana daga cikin kasashen da coronavirus ta addaba a nahiyar Turai.
A ranar Talata mahukunta suka ce mutum 2,696 ne suka mutu, yayin da 40,000 suka kamu da coronavirus.

Asalin hoton, Getty Images
Yankin Catolinya shi ne daya daga wurin da cutar ta fi yi wa illa.
An ruwaito cewar Lionel Messi da Cristiano Ronaldo kowanne ya bayar da gudunmuwar Yuro miliyan daya domin yakar coronavirus a makon jiya.
Mundo Deportivo ta ce dan wasan Barcelona, Messi ya bai wa asibiti biyu kudi da ya kai Yuro milayan daya don yakar cutar daya a Barcelona dayan kuma a Argentina.

Asalin hoton, Getty Images
Shi kuma dan kwallon Juventus, Ronaldo da mai kula da wasansa, Joege Mendes sun bayar da Yuro miliyan daya ga cibiyoyin yaki da coranavirus uku, domin taimakawa mutane.
A makon jiya dan kwallon Bayern Munich, Robert Lewandowski ya bayar da taimakon Yuro miliyan daya don yakar cutar a Jamus.











