An dakatar da Champions da Europa League

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa ta dakatar da dukkan wasannin Zakarun Turai na Champions da na Europa League saboda coronavirus.

Hukumar ta kuma dage gasar kasa da kasa har da wasan cike gurbin cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020 - wadda tuni aka ce sai a 2021 za a gudanar.

Tuni kuma ta soke dukkan wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai a kwallon mata da za a gudanar da gasar a 2021.

Mambobin hukumar kwallon kafar Turai 55 ne suka cimma matsaya, bayan da suka gudanar da taro ranar Laraba.

Ana sa ran ci gaba da buga gasar Premier zuwa 30 ga watan Afirilu, idan an ga karshen coronovirus.

Wadan da ya kamata su buga wasannin cike gurbin shiga gasar nahiyar Turai ta 2020 sun hada da Ireland ta Arewa da Jamhuriyar Ireland da kuma Scotland.

Kungiyoyin Premier da ke Champions League sun hada da Manchester City da Chelsea, yayin da Manchester United da Wolves ke buga Europa League.

An dage dukkan wasan karshe da ya kamata a buga a watan Mayu a kofin Champions League da Europa da kuma na mata na Zakarun kungiyoyin Turan.