Asante ta fitar da Pillars a Zakarun Afirka

Asalin hoton, Malikawa
Asante Kotoko ta Ghana ta yi nasara a kan Kano Pillars da ci 2-0 a wasan share fagen gasar cin kofin Zakarun Afirka ta Champions League.
Asante ta ci Pillars mai wakiltar Najeriya kwallo 2-0 a Ghana a wasa na biyu da suka fafata ranar Lahadi.
A wasan farko da suka kara a Najeria, Pillars ce ta yi nasara da ci 3-2 a fafatawar da suka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano, Najeriya.
Jumulla Asante ta ci kwallo 4-3 kenan gida da waje, hakan ne ya kai ta karawar zagayen gaba a gasar ta Zakarun Afirka wato Champions League.
Pillars ta samu gurbin buga gasar CAF ta bana ne, bayan da ta yi ta biyu a gasar Premier Najeriya da aka kammala wadda Enyimba ta lashe kofin.
Haka kuma Pillars din ita ce ta lashe kofin kalubalen kasar a bana wato Aiteo Cup, tun bayan da ya dade rabonta da shi.







