Lafiya Zinariya: Cutar kansar da ake iya yi wa riga-kafi

Saurari hirar da Fauziyya Kabir Tukur ta yi da Dokta Zainab Shinkafi-Bagudu kashi na ɗaya da na biyu kan kansar bakin mahaifa

Kansar bakin mahaifa na samuwa ne a daidai bakin mahaifar mace, wato mashigar mahaifarta.

Wannan cuta ta fi shafar matan da ke jima'i musamman wadanda ke tsakanin shekarun 30 zuwa 45. Yawanci maza ne ke dauke da ƙwayar cutar a jikinsu wadda kan janyo masu wasu irin ƙuraje a baki.

Amma ida namiji mai dauke da wannan ƙwayar cuta ya sadu da mace lafiyayya tana iya ɗaukar wannan cuta har ta zamar mata kansa a bakin mahaifarta.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce ita ce kansa ta huɗu mafi shahara a mata.

A shekarar 2018, an yi kiyasin cewa mata 570,000 suka kamu da ita a faɗin duniya kuma a cikin matan guda 311,000 ne suka mutu sanadiyyar cutar.

Amma shekaru goma sha biyar da suka gabata, an gano riga-kafin wannan cuta wadda ke iya bai wa mata kariya daga kamuwa da ita.

Alamomin kansar bakin mahaifa

Bincike ya nuna cewa daga farko-farko kansar ba ta nuna wasu alamomi.

Amma alamomin da aka fi gani su ne:

Zubar da jini a lokacin da ba na al'ada ba, kamar lokacin saduwa ko bayan saduwa.

Haka kuma, matan da suka kai shekarun daukewar jinin al'ada kan ga zubar jini.

Duka waɗannan alamomi ne na kansar bakin mahaifa amma an fi so a je asibiti idan aka ga waɗannan alamomin saboda a wasu lokutan wasu cutukan ne na daban.

Me ke janyo kansar bakin mahaifa?

Ƙwayar cuta ta HPV ita ta fi haifar da wannan cuta.

HPV wata ƙwayar cuta ce da ake iya saurin yaɗawa ta hanyar saduwa tsakanin mace da namiji.

Ana iya magance wannan kansa idan aka gano ta da wuri shi ya sa ake so mata su riƙa zuwa asibiti ana tantance su a kai a kai.

Tantancewa na bayar da damar gano cutar da wuri kuma a hana ta yaduwa.

Amma idan har cutar ta yi yawa a bakin mahaifar, ana iya yin tiyata a yanke mahaifar gaba ɗaya sannan a yi gashin radiotherapy don ƙone ƙwayoyin cutar.

Riga-kafin cutar kansar mahaifa

Ƙwararru sun gani riga-kafin cutar kansar mahaifa wadda ke bai wa mata kariya daga kamuwa da wannan cuta.

Haka kuma, ana iya yi wa maza wannan allurar don hana ƙwayar cutar yin tasiri a jikinsu sannan ta hana su yaɗawa ga matansu.

An fi so a yi wa yarinyar mace da ba ta haura shekara 9 ba wannan allura, wannan na nufin a lokacin ba ta riga ta fara saduwa da namiji ba.

Ga matan da suka fara saduwa, likitoci na ba da shawarar su riƙa zuwa asibiti ana tantance su duk bayan shekara 3 don tabbatar da cewa ba sa dauke da cutar.