Lafiya Zinariya: Cutar da ke sa mata gemu da mayar da muryarsu kamar ta maza

Ku latsa lasifikar da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar Fauziyya Kabir Tukur da likita kan hakan:

Polycystic Pvarian Syndrome ko PCOS na daya daga cikin manyan abubuwan da ke hana mata haihuwa, sannan take bai wa mata wasu na'ikan jikin maza.

Har yanzu ba a gano takamaiman abin da ke haifar da wannan cuta ba, amma likitoci na ganin cewa ana gadon ta.

Cuta ce da ke fara bayyana a lokacin da 'ya mace ta balaga, wato ta soma jinin al'ada kuma a kan gano a lokacin amma a wasu ba a sanin cewa da wannan cuta har sai mace ta yi aure ta fara neman haihuwa.

Dakta Surayya Awwal Sulaiman, ta babban asibitin Tarayya da ke Abuja a Najeriya ta yi bayani kan wannan cuta da illolinta a jiki da kuma irin taimakon da ake bai wa masu fama da ita.