Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Matsalar cutar damuwa ta yi matuƙar tagayyara rayuwata
Ku latsa hoton da ke sama don sauraron hirar Fauziyya Kabir Tukur da matar da ta haɗu da lalurar kashi na farko da na biyu:
Cutar tsananin damuwa na daya daga cikin nau'ukan cututtukan da ke shafar lafiyar ƙwaƙwalwa a ɗan Adam.
Kuma Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce tana daya daga cikin manyan lalurori da ka iya zama babbar barazana ga lafiyar ƙwaƙwalwa idan ba a magance ta ba. Asali ma, hukumar ta ce ta kan janyo masu fama da ita su iya kashe kansu.
Ladi (ba sunanta na ainihi ba) da ta yi fama da wannan cuta, ta bayyana cewa ita jaririnta dan wata bakwai ne ta so ta hallaka.
"Idan aka kawo min ruwan zafi zan yi masa wanka, sai in ji kamar in jefa shi a cikin ruwan nan kafin a surka. Kawai wai don in ga yadda zai yi," a cewarta.
Ta kuma ce ba ta san dalilin da ya sa ta ke wannan tunanin mara kyau ba.
"Ba mugunta nake so in yi masa ba, kawai ni ma ban san abin da ya sa nake wannan tunanin ba. Na sha tunanin in wurga shi daga saman bene ma, haka kawai don in ga yadda mutum ke karerayewa," a cewa Ladi.
Kiyasin da WHO ta yi, ya nuna cewa a kalla mutum miliyan 264 ne cutar ke kamawa a fadin duniya, kuma tana kama manya da yara da maza da mata.
Sai dai alkaluman sun nuna cewa ta fi kama mata.
Akwai abubuwa da dama da ke iya haifar da cutar tsananin damuwa, amma kwararru na ganin cewa sau da yawa, wasu abubuwa da ke faruwa a rayuwar mutum kamar rasa aikin yi ko rashin wani makusanci ko fuskantar hatsari ko faruwar wani mummunan al'amari na haifar da tsananin damuwa har ya zama cuta.
Wasu shirye-shiryen na baya da za ku so ku saurara
Ga Ladi, zaman aure mai cike da ruɗani da rasuwar mahaifiyarta da suka yi matukar shaƙuwa ne suka haifar mata da wanann cuta.
"Aurena na farko da na fuskanci duka da sauransu bayan na fito sai na fara ganin wasu alamomi kamar idan ina bacci sai in ji kamar an tashe ni. Idan na leka ta taga sai ba zan ga kowa ba.
"Na yi nadamar rashin rama abubuwan da mijina na farko ya yi min sai na shiga tsananin damuwa," in ji Ladi.
"Bayan rasuwar mahaifiyata kuma sai in shiga daki ni kadai in kashe wuta, sai in ga kamar za ta zo ta yi min magana. Sai ma na fara ganinta tana min magana har ta fadi abin dariya in yi dariya," in ji ta.
Ladi ta ce su kan yi hira sosai da mahaifiyarta da ta rasu, abin da ya ankarar da 'yan uwanta su ka fahimci akwai tsananin damuwa a tare da ita.
"Da sun dauka ba ni da dangana ne, sai ai ta min fada a ce na ki in hakura. Amma daga baya sai aka kai ni asibiti. Aka ce ina da hawan jini kuma amma ba ya sauka ko an ba ni magani."
"Sannan ga matsanancin ciwon kai, kuma ba na iya bacci. Daga baya na je asibitin masu fama da matsalar kwakwalwa a nan ne aka ce min ina da cutar tsananin damuwa."
WHO ta ce ga masu fama da cutar, su kan zama kamar masu nakasa saboda tagayyara su da cutar ke yi.
Akwai magungunan da ake ba masu fama da wannan cuta don su samu sauki kuma su ci gaba da rayuwarsu yadda suka saba a baya, amma samun kulawa da goyon baya daga 'yan uwa da makusantan mai fama da lalurar na taimakawa sosai wajen samun lafiya.