Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Abubuwa biyar da za su kare ku daga kamuwa da sankarar mama
Ku latsa alamar lasifika da ke sama don sauraren Lafiya Zinariya wanda Fauziyya Kabir Tukur ta gabatar. Wannan shirin ci gaban wanda muka gabatar ne a makon jiya. Don haka mun sa musu suna Lafiya Zinariya mako na farko da Lafiya Zinariya nako na biyu
Sankarar mama ita ce cutar daji da mata suka fi fama da ita inda take shafar akalla mace miliyan biyu da dubu dari daya duk shekara, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.
Haka kuma, hukumar ta ce ita ce cutar da ta fi janyo mace-macen da suka danganci cutar daji a mata.
Amma hukumar ta ce idan aka gano ta da wuri, ana iya warkewa daga cutar ta sankarar mama.
Shi ya sa ma ake yawan bai wa mata shawarar yin gwaji akai akai.
Baya ga wannan, ga wasu abubuwa biyar da WHO ta ce idan aka bi ƙa'idarsu ana iya gujewa kamuwa da sankarar mama.
1. Daina shan taba sigari: A fadin duniya, taba sigari ita ce dabi'a daya tilo da idan aka guje mata ake iya kaucewa shiga hadarin kamuwa da cutar daji. Tana kasha a kalla mutum miliyan 6 duk shekara. Taba sigari na da sinadarai masu hadari sama da 7000 kuma fiye da guda 50 daga cikinsu na janyo cutar sankara ta ko wane bangare na jiki. Shanta na janyo cutar daji a huhu da ciki da makogwaro da mama da koda da hanta da sauransu.
2. Cin abinci mai gina jiki da yawan motsa jiki na bayar da kariya daga cutar daji. Bincike ya nuna cewa mata masu kiba sun fi hadarin kamuwa da sankarar mama. Amma cin abinci mai dauke da kayan lambu da kayan marmari na gyara garkuwar jiki da inganta yadda jiki ke sarrafa sinadarensa. Yawan motsa jiki da tabbatar da cewa ba a saki teba ba na rage hadarin kamuwa da cutar dajin.
3. Shan barasa na cikin abubuwan da ke jefa mata cikin hadarin kamuwa da cutar sankarar mama. Wani bincike da aka gudanar a 2010, WHO ta ce a kalla shan barasa na janyo mutiwar mutane 337,400 ta hanyar cutar daji a fadin duniya.
4. Gurbacewar muhalli na daga cikin abubuwan da ke haifar da cutar daji. Gurbatacciyar iska da gurbataccen ruwa da gurbatacciyar kasar noma na kara jefa mutane cikin hadarin kamuwa da sankara. WHO ta yi kiyasin cewa gurbatacciyar iska na janyo mutuwar akalla mutum miliyan uku da dubu dari biyu.