Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Abubuwan da ke jawo ƙaiƙayi a al'aurar mata
Latsa hoton da keƙasa don sauraron shirin:
Hukumar dakile yaduwar cutuka ta Amurka, CDC ta ce matsalar kaikayin gaban mata na daya daga cikin cutukan da likitoci suka ce suna yawan kai mata a fadin duniya asibiti.
Kashi 75 cikin 100 na matan da ke duniya za su gamu da matsalar kaikayin gaba akalla sau daya a rayuwarsu a cewar hukumar.
Sai dai ta ce wannan matsala na da saurin warkewa idan aka yi amfani da magungunan da suka dace.
Kaikayi da radadi a lokacin yin fitsari ko saduwa, fitar ruwa mai yawa ta gaba da kuraje na daga cikin alamomin cutar, kamar yadda Dakta Anisa Umar Ambursa, ta asibitin Federal Medical Centre da ke Jabi a Abuja babban birnin Najeriya, ta yi bayani.
Sannan likitar ta yi bayani kan wasu dabi'u da mata ke yi da ke iya haifar da wannan matsala.