Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: 'Yadda na rayu da cutar PCOS kuma na yi nasara'
A mafi yawan al'adu a fadin duniya, ana yi wa macen da ba ta haihu ba kallon ba ta kai ta kawo ba.
A wasu al'adun ma a kan goranta mata ko da kuwa wata matsala ko cuta ce ta hana ta haihuwar.
Ilimin kimiyya ya nuna cewa abu ne mai wuya mace ta iya haihuwa idan ba ta jinin al'ada saboda shi ne ginshikin samuwar ciki a gareta.
Kwan haihuwar mace da ke samuwa a ovary da ke mararta ke zama jinin al'ada idan bai hadu da kwan haihuwa na namiji ba, kamar yadda shafin intanet na hukumar Inshorar lafiya ta Burtaniya ya wallafa.
To a lokacin da ya kasance kwan halitta ba ya samuwa a marar mace, ba za ta samu jinin al'ada ba kuma daukar ciki zai yi wahala a gareta.
Daya daga cikin abubuwan da ke haifar da wannan matsala ita ce cutar PCOS wadda ke shafar ovary da ke mararta.
Wata mata, wadda ba ta amince a bayyana sunanta ba ta ba da labarin yadda ta fara gano cewa tana da cutar PCOS lokacin tana 'yar shekara 12 a duniya.
Ta bayyana gwagwarmayar da ta sha da rashin haihuwa da sauran illilon da wannan cuta ta yi wa lafiyarta.