Lafiya Zinariya: Cutar PID da ka iya hana mata haihuwa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Cutar PID (pelvic inflammatory disease) na daya daga cikin cutukan da ke addabar daruruwan mata a fadin duniya, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce.

A cewar hukumar, wannnan cuta ta danganci cutukan da ake iya samu dalilin saduwa kuma rashin yin maganinta na iya sawa mace ta gamu da matsalar da za ta iya hana ta haihuwa. Hakan na nufin namiji na iya bai wa mace cutar idan ya sadu da ita.

Sai dai kuma akwai wasu abubuwan na daban da ke iya janyo cutar da ba saduwa ba.

Duk da cewa akwai cutuka da dama da mata ke iya dauka ta hanyar jima'i, cutar PID na daya daga cikin wadanda aka fi gani a mata, amma kuma mata da dama ba su cika ganin alamominta ba har sai ta yi wa jikinsu illa.

A wannan makon, Dakta Maryam Fadila Isa ta yi bayani dangane da haka kuma ta bai wa mata har ma da maza shawarwari dangane da cutar ta PID.