Algeria: 'Sayen mai girki ya kasance tamkar sayen magani'

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Daga Rachid Sekkai
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
Ana ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayayyaki a Algeria, inda masu kantuna suka ce man girki da madara sun yi karanci sai ka yi da gaske kafin ka samu.
Tasirin matakan da aka dauka saboda bullar annobar korona da kuma yakin Ukraine na sake jefa rayuwa cikin tsanani ga jama'ar kasar.
"Kamar muna sayen magani," a cewar Samiha Sammer, mai shekara 31, cikin yanayi na nuna takaici.
Tana sana'ar sayar da kek ga 'yan uwanta da abokai, wani lokaci ma tana ɗan samun abin kashewa daga wannan sana'ar, sai dai a yanzu ba ta iya samun abubuwan da take bukata don hada kek din.
"Kafin ka iya sayen mai daga kowanne kantin sayar da kayayyakin amfanin gida, sai akwai sanayya tsakaninka da mai shago ko kanti," a cewar Sammer.
Ana gudanar da hakan ne cikin yanayi na taka-tsantsan, inda ake boye wasu kayayyakin a bayan kanti.
Ita da wasu 'yan Algeria sun ce abubuwa sun sauya a shekarar da ta gabata, lokacin da matakan yaki da annobar korona suka yi tsanani.
A yanzu, da watan Azumin Ramadana ke karatowa, 'yan Algeria sun matsa kaimi wajen ganin sun tanadi man girki kasancewa abu ne mai muhimmanci wajen hada abinci a lokacin Ramadan.
Sammer takan yi tafiya tsakanin gidanta a Bilda zuwa garuruwa makwabta irin su Kolea, inda ake samun kayan marmari da itatuwa cikin rahusa.

Asalin hoton, Samiha Sammer
A kwanakin nan farashin dankali ya karu da kashi 30 cikin 100 tsadar ta yi tsanani idan ka duba yadda ake saye a watannin baya, dogayen layin da ake gani wajen sayen madara na nufin mutane na yini a kan layi kafin samun madara su kai gida.
"Yanzu a daina yin haka saboda turereniyar da ake yi ga cunkosa wani lokaci har fada ake yi saboda neman madara," kamar yadda wani ma'aikaci yake cewa cikin yanayi na damuwa. "Yanayin abin kunya ce."
Kuma idan ka yi kokarin kauracewa bin layi to aljihunka zai amsa.
A yanzu tana biya kusan kudin kasar dinar 420 kan kilo 1 na madarar gari da ake shigowa da shi maimako dinar 25 na rangwamen da muke samu.
Algeria na samar da madara amma cikin kason ba shi da yawa, don haka tsawon shekaru ta dogara ne kan madarar da ake kai mata daga Faransa, da saura kasashen Turai da kuma na baya-bayan nan daga Hadaddiyar Daular Larabawa - akasari madarar ta gari ce.
Sai dai abin da ya fi damun 'yan Algeria shi ne batun man girki.
Kamar yadda suke samun tallafi kan madarar da suke saye, shi ma aka man girki yake, sai dai tun kafin rikicin, da ma man ya yi tsada - ana sayar da lita biyar na mai kan dinar 600 ($4.20; £3.20).

Asalin hoton, Getty Images
Idan aka kwatanta da matsakaicin albashin ma'aikaci na dala 240 ga ma'aikatan kamfanoni masu zaman kansu da dala 410 na ma'aikatan gwamnati, matsin na kara fitowa fili na bukatar mahukunta su tashi tsaye.
Rike abinci da rashawa sun karu yayinda matsalolin tattalin arziki ke galabaita mutane, kamar yadda rahoton kwamitin da majalisa ta kafa ke nunawa.
Mamba a kwamitin Hishan Safar ya shaida wa BBC cewa masu sayar da man girki sun kara kudi ne saboda su maido da kudadensu da gwamnati ta janye na tallafi.
A shekarar da ta gabata, kusan mutum 150,000 aka ba da rahoton sun karya dokar mahukunta, wanda akasari suka karkare a kotu, kuma an kwace lasisin mutane da dama da ke sana'a.
Sai dai akwai kuma matsala wajen fasa-kaurin kayayyakin abinci mai rahusa ta iyakokin kudancin Algeria don sayarwa kasashe makwabta, wanda kwamitin majaisa ke cewa ya "ta'azzara".
Babu alkaluma a hukumance amma majiyoyi sun shaidawa BBC ce akwai manyan motoci da yawansu ya kai 12 cike da man girki ana fasa-kaurinsu daga Algeria zuwa Mali da Nijar a kullum.
Masu aikata hakan na sayar da kayayyakin da gwamnati ke bayarwa kan farashi mai rahusa, man girkin da ake yi a Algeria a kudaden ketare - ana samun ribar kusan dala 17,800 a kowacce mota guda, kamar yada majiyoyi suka shaidawa BBC.
A farkon wannan watan, Shugaba Abdelmadjid Tebboune ya haramta fitar da kayayyain abinci da ke kunshe da sinadaran da aka shigo da su - irinsu man girki da sukari da taliya da garin semalina da alkamana.
Rahotanni na cewa shugaban na son a hukunta masu aikata hakan saboda suna yiwa "tattalin arzikin kasar zagon-kasa".
Amma domin gane ainihin abin da ke haddasa waɗannan matsaloli a Algeria dole sai an yi waiwaye, a cewar kwararu.
'Mafiyoyi na sace kadarorinsa'
Tattalin arzikin kasar da ya dogara kan sayar da gas da ɗanyen man fetur wanda ke kawo musu riba da hayar samun kudaden shigar gwamnati, a yanzu na zame musu matsala, a cewar masanin tattalin arziki Abdal-Rahman Hadef.
Cin karensu babu-babbaka a harkokin tafiyar da gwamnati da tattalin arziki na ɗaiɗaita harkokin kasuwanci, da hauhawar farashi a cewar Mista Hadef.
Akwai kuma damuwar cewa tattalin arzikin kasar na iya jefa kasar cikin ukubar rikicin siyasa.

Asalin hoton, AFP
An tilasta wa tsohon Shugaba Abdelazziz Bouteflika sauka daga mulki a 2019 a wani bore da 'yan kasar suka yi.
Wanda ya gaje shi, wanda ya taba zama makusancinsa, a yanzu ya yi Alla-wadai da mafiyoyin da ke "wawushe dukiyar kasar" karkashin mulkin Bouteflika.
Duk da sauyin gwamnatin da aka samu, mutane da dama sun kasance cikin fushi da ci gaba da zanga-zanga har bullar annobar korina a Maris din 2020.
Kashi daya ciki uu na 'yan kasar ba su zarta shekara 37 ba a duniya, kuma rashin aikinyi ya kai kashi 11 cikin 100 na al'ummar kasar, wanda galibinsu matasa ne da suka kammala jami'a.
Yayinda aka sa ido sosai, gwamnati na cewa daga wannan watan, duk masara aikinyi da suke iya nuna cewa suna da gwazon aiki za su ke samun dala 90 a kowane wata a matsayin alawus.
Sai dai zance na zahiri, tsadar da gas ta yi a kasuwar duniya saboda yakin Ukraine ya taimakawa mahukunta kasar wajen iya samun kudin biyan wannan alawus na gajeren lokaci.
Amma masana tattalin arziki na nuna dagewa kan Algeria ba za ta iya cigaba da biyan waɗannan kudade ba nan gaba.
Amma a matsayin da ake ciki a yanzu, masu sayayya irinsu Ms Sammer na cikin tsaka-mai-wuya na iya tantace me za su saya domin amfanin yau da kullum.











