Duka da zubar da ciki: Rayuwa a gidan yarin Koriya Ta Arewa

Wata ƙungiya ta nuna yadda ake tsare da mutane da ɗaya daga cikin gidajen yariin Koriya Ta Arewa.

Asalin hoton, Korea Future

Bayanan hoto, Wata ƙungiya ta nuna yadda ake tsare da mutane da ɗaya daga cikin gidajen yariin Koriya Ta Arewa.
    • Marubuci, Daga Laura Bicker
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC, Seoul

Bayan ta shiga ɗakin da ake tsare da ita, an umurci Lee Young-joo ta zauna ta lanƙwashe gwiwowinta da hannayenta a guiwa.

An hana ta tashi na tsawon sa'a 12 a rana.

Ba ta samun isshen ruwa kuma an takaita mata yawan abin da za ta ci.

"Ina jin kamar an mayar da ni dabba, ba mutum ba," in ji ta.

"Ta faɗa wa BBC ta shafe awanni tana fuskantar tambayoyi kan abin da yawancin mutane ba su damu da shi ba - barin ƙasarta. Ta yi ƙoƙarin tserewa daga Koriya ta Arewa a 2007 kuma an kamata a China aka mayar da ita.

Ta shafe wata uku a cibiyar da ake tsare mutane a Koriya Ta Arewa kusa da kan iyaka da China, tana jiran hukunci.

A yayin da take zaune a ɗakin da ake tsare da ita tana sauraren takun takalmin masu gadi "kulak kulak kulak" a lokacin da yake sintiri.

Yana gaba yana baya. A yayin da ƙarar takun ta fara gushewa, Young-joo ta samu dama ta yi wa ɗaya daga cikin abokin zamanta magana.

"Za mu yi magana kan dubarun sauya sheƙa, tsarin yadda za mu haɗu da wakilai, wannan magana ce ta siri."

Gidan yari ya kamata ya zama dalilin hana mutane tserewa daga Koriya Ta Arewa - amma hakan bai yi aiki ba ga Young-joo da kuma abokan zamanta a gidan yarin. Yawancinsu suna jiran a yanke masu hukunci kan koƙarin barin ƙasarsu.

Amma an saurari tsarin Young-joo.

"Jami'in tsaron gidan yarin zai kira ni ya ce na ɗora hannu na, ya fara duka na a hannu da abin makulli har sai ya sauya launi.

Ba na son yin kuka saboda alfahari. Waɗannan masu tsaron gidan yarin sun ɗauke mu waɗanda ke son guduwa daga Koriya ta arewa a matsayin masu cin amana.

"Za ka ji ana dukan wasu saboda a wuri ɗaya ne. Ina ɗaki na uku amma ina jin dukan ɗaki na 10."

Tsarin kawo ƙarshe

Young-joo na cikin mutum sama da 200 da suka taimaka da bayanai a binciken kungiyar makomar Koriya wato Future Korea na keta dokokin duniya a tsarin gidajen yarin Koriya Ta Arewa.

Ƙungiyar mai zaman kanta ta gano masu laifi 597 da ke da alaƙa da laifuka 5,181 na keta haƙƙin ɗan adam da aka aikata kan waɗanda ake tsare da su a 785 a wurare 148.

An tattara hujjojin aka adana da nufin wata rana waɗanda ke da laifi za a hukunta su.

Koriya Ta Arewa ta daɗe tana musanta aikata laifukan keta haƙƙin ɗan Adam. BBC ta yi ƙoƙarin tuntuɓar wakilai daga ɓangaren Koriya Ta Arewa domin mayar da martani kan wannan binciken amma babu amsa.

Ƙungiyar ta kuma samar da wata na'ura ta 3D a cibiyoyin tsare mutane domin ba mutane damar ganin halin da suke ciki.

Wata ƙungiya ta nuna yadda ake tsare da mutane da ɗaya daga cikin gidajen yariin Koriya Ta Arewa.

Asalin hoton, Korea Future

Daraktan Ƙungiyar Korea Future a Seoul, Suyeon Yoo ya shaida wa BBC cewa tsarin gidan yari da kuma rikicinsa ana amfani da shi ne domin "koƙarin rage yawan mutane miliyan 25.

"A duk hirar da muka yi, muna ganin yadda wannan ke tasiri ga rayuwar mutane. Ɗaya daga cikin wanda muka yi hira da shi ta bayyana damua yayin da ta tuna yadda aka kashe jinjirin da aka haifa. "

Zarge-zarge da dama kan cin zarafi

Koriya ta Arewa ta fuskantar wariya a duniya fiye da baya.

Gidan Kim ke shugabantar ƙasar tsawon shekaru, kuma ƴan ƙasarta dole su nuna goyon baya ga gidan da kuma shugabanta na yanzu Kim Jong-un.

Annobar korona ta sa an tsaurara matakai a ciki da kan iyakokin ƙasar.

Akwai hukunci mai tsauri kan waɗanda suka yi tunanin fita - sun haɗa da waɗanda ke kallon fina-finan ƙasashen waje.

Akwai zarge-zarge da dama na fyaɗe da sauran nau'in cin zarafi. Waɗanda suka tsira sun faɗa wa ƙungiyar cewa ana tilasta masu zubar da ciki.

A arewacin lardin Hamgyong, wata da aka yi hira da ita ta ce ta ga yadda aka tilasta wa wata zubar da cikinta na wata takwas. Ta yi iƙirarin cewa yaron ya tsira amma aka jefa shi cikin ruwa.

An samu bayanai da dama a binciken daga mutanen da aka taba tsarewa a wurin tsare mutane a Onsong

Asalin hoton, Korea Future

Bayanan hoto, An samu bayanai da dama a binciken daga mutanen da aka taba tsarewa a wurin tsare mutane a Onsong

Akwai wurare biyar da shaidu suka bayyana ana kashe mutane.

Samun adalci

Young-joo an yanke mata hukuncin shekara uku da rabi a gidan yari.

"Na damu kan cewa zan rayu zuwa lokacin da na kammala wa'adin da aka yanke min," in ji ta. Idan ka shiga irin waɗannan wuraren, dole ka fitar da ran samun rayuwa," a cewarta.

Saerom ma na cibiyar tsare mutane ta Onsong a 2007, amma ta tuna dukan da aka yi mata a hannun jami'an tsaro na sirri da ya yi muni.

"Suna dukanka da icce mai kauri, kana kuka. Ban damu da sauran mutane yadda ake dukansu ba, idan na kawar da kai na za su sake juyo da ni na kalla."

"Idan akwai wata hanya, ina son a hukunta su," kamar yadda Sarom ta faɗa muna yayin da take nuna halin ƙuncin da ta shiga a gidan yari.

Yanzu ta ce tana girmama duk wani farin ciki na sabuwar rayuwarta a Koriya ta Arewa."

Hukunta waɗannan laifukan zai yi wahala, amma binciken ya samar da wata hanya daga masana na kotun hukunta manyan laifuka. Hujjojin za a iya amfani da su a kotu kuma an samar da su ba shamaki.

Saerom da Young-joo dukkaninsu sun shaida muna cewa suna fatan wannan rahoton zai taimaka a yi fitar masu da haƙƙinsu ya kai ga samun adalci.