Mutanen da aka hukunta saboda sun faɗi abin da ke damunsu a wurin aiki

    • Marubuci, Daga Zulekha Nathoo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Worklife

Kowane wurin aiki na da irin na sa hanyoyin mu'amalar da ma'aikata ke bi wajen bayyana yadda suke ji a kan komai da kuma yadda ya kamata su yi. Ana kiran su "dokokin zuci", kuma sun mamaye wuraren aiki sosai ta yadda ba a wani mayar da hankali a kan su.

Misali, idan abokin aiki ya sanar cewa an saka ranar aurensa, dokokin zuci sun tanadi cewa murna za a yi. Idan kuma shugabanku (a wurin aiki) ya ce tawagarku ta yi asara, ana ganin abin da ya dace a nuna ɓacin rai ko fiushi.

Sai dai ba duka hanyoyin bayyana abin da mutum ke ji ba ne ke samun karɓuwa ba; masana sun ce abin da ya kamata da wanda bai kamata a ce ba ya danganta ne da ma'aikacin. Mun san cewa ana yi wa macen da ke ɗaga murya a wajen aiki kallon mafaɗaciya, yayin da kuma ake wa namiji mai irin wannan halin kallon mai iko ko kuma shugba.

Sai dai, bincike ya nuna cewa babu maganar jinsi a dokokin zuci - akwai kuma bambancin launin fata. Bayanai sun nuna idan ma'aikata da ba fararen fata ba suka faɗi abin da suke ji zai iya jawo wani abu daban idan aka kwatanta da na fararen fata kan wannan abin.

Hakan ta sa ma'aikatan BIPOC suke kaffa-kaffa da motsinsu a wurin aiki don kare kansu daga yadda wasu ke fassara halayensu waɗanda zai iya shafar aikinsu ta mummunar hanya - kuma hakan na ƙara yawan nauyi a ƙwaƙwalwarsu.

'Ka ga irin wannan kallon'

A tsawon shekaru, bincike-bincike sun nuna yadda ake amfani da dokokin zuci ta hanyoyi daban-daban kan maza da mata. Wanda aka fi yi shi ne mutane kan yi wa mace hukunci kan fushi ko ɓacin ko kuma gazawa mai tsauri fiye da namiji a kan abu ɗaya.

Masu binciken sun gano cewa mata da suke kuka a wurin aiki ana kallonsu a matsayin masu rauni, su kuma maza ana ganin suna yin nasu kukan ne ta hanyar wasu ɓangarorin da suka fi kuka girma. Kazalika, mazan da ke nuna fushi kan amfani da hakan wajen nuna cewa masu iko ne yayin da mata kuma ake musu kallon fanko - ba su san aiki ba.

A wani bincike na 2014, ɗaliban digirin farko a jami'a 170 sun kalli wani bidiyo na jawabin wasu lauyoyi na ƙarshe a wata shari'a. An nemi ɗaliban su yi hukunci tare bai wa lauyoyin maki game da kwarearsu. Lauyoyi maza da suka fi nuna fushi sun samu maki mai yawa, yayin da aka bai wa lauyoyi mata da suka nuna fushi maki mafi ƙaranci. Bugu da ƙari, ɗaliban sun alaƙanta fushin da matan suka nuna da rashin ƙarfin zuciyarsu amma kuma suka alaƙanta na mazan da cewa lamarin ne ya sa suka yi fushin.

Abu ne mawuyaci a iya tantance ainahin abin da ke jawo bambancin jinsin, to amma za a iya dora laifin hakan a kan al'ada da kuma rashin saba ganin mata a matsayi na shugabanci, sai dai a mtsayi na tallafa wa shugaba ko shugabanci.

A kwanan nan wani bincike da aka yi ya nuna irin wannan matsala game da yadda mutane ke daukan yanayin da bakaken fata da sauran tsirarun mutane wadanda ba ainahin Turawa ba (BIPOC) ke ji a wurin aiki idan aka kwatanta su da takwarorinsu Turawa

Ko da ma'aikata sun bi ka'idar bayyana yadda suke yi, sheda na nuna cewa, ma'aikata bakaken fata da sauran tsirarun jinsi, musamman ma dai bakaken dole ne su jure irin yanayin da suke ciki ko kuma su dandana kudarsu.

Robert, wanda bakar fata ne kuma babban jami'i a wata kafar yada labarai a Birtaniya ya ce idan yana cikin tsananin nishadi a wurin aiki a kan maganar wani aiki, wadanda suke kusa da shi a yawancin lokaci sai su yi masa wata fassara ta daban da niyyarsa.

"Ina gani a yanayinsu da kuma idanuwansu cewa suna jin tsorona, idan ina cike da shauki.'' In ji Robert wanda aka boye daya sunan nasa domin a kare aikinsa kada abin da ya fada ya shafe shi.

Ya kara da cewa: "Ina ganin idan kai bakar fata ne, mutane da yawa suna jin tsoronka. Da ka dan daga muryarka, za ka ga yadda ake kallonka. Mutane ba sa cewa komai, amma za ka ga suna cikin tsoro."

Masu bincike sun ce abin da ke faruwa ga Roberts yana faruwa akai-akai a wuraren aiki da kuma a tsakanin mutane yau da kullum.

Wani bincike da aka wallafa a watan Afrilu wanda Stephanie Ortiz, farfesa a fannin ilimin halayyar dan-Adam a jami'ar UMass Lowell da ke kusa da Boston, ya nuna yadda ake da bambanci sosai wajen aiwatar da dokokin bayyana yanayin da ma'aikaci yake, musamman a kan jinsi.

Ortiz ta yi hira da malamai a wuraren tattaruwar 'yan luwadi da madigo na makarantu a Amurka.

Tambayoyin da ta yi sun kunshi yadda shugabanni suke daukar yanayin da masu luwadin da ire-irensu ke ciki a lokacin da ma'aikata suka yi kokarin tattauna batutuwan wariyar launin fata da wariyar da ake nuna musu idan daliban suka fada musu halin da suke ciki a sirrance.

Bincike ya nuna cewa ma'aikata farar fata wadanda suka nuna bacin rai a gaban shugabanni a madadin sauran dalibai, ana daukar wadannan a matsayin wadsanda suke da matukar saha'awar aikinsu.

To amma kuma idan ma'aikatan da ba ainahin Turawa ba ne, idan suka yi irin wannan halayya sai a ce masu tsattsauran ra'ayi ne, ba a daukarsu a matsayin abokan tafiya idan sun bayyana bacin ransu, a madadin daliban da ake nuna musu wariya da bambanci.

Masu binciken sun zartar da cewa ana nuna wariya inda ake fassara yanayi ko halin da ma'aikata bakar fata da sauran tsiraru marassa rinjaye ke ciki a matsayin ''bacin rai'' amma kuma ma a wurin da yake ma'aikata farar fata sun fi yawa ake daukar hakan a matsayin babbar barazana, idan bakaken suka yi sabanin idan fararen fata ne suka yi.

A dalilin haka ma'aikata bakar fata da sauran tsiraru wadanda ba Turawa ba, a yawancin lokaci sai sun dage sun nuna ainahin yanayin halin da suke ciki a lokacin tattauna wani batu da ya shafi jinsi da rashin daidaito, idan ba haka ba sai a rika fassara su a matsayin makiya ko abokan gaba.

Idan ya kasance bakakr fatan ba sa yin haka to sai a rika daukarsu a matsayin masu neman wanzar da wata manufa ko kuma dabi'ar da ta saba wa aiki, in ji Chad Mandala, dalibin karatun digirin digirgir a jami'ar Georgia, wanda yake aiki tare da Ortiz a nazarin

Masaniya kan halayyar dan-Adam Adia Wingfield, a bincikenta a kan dokokin yadda mutane ke ji ko halin da mutane ke ciki, ta nuna cewa ma'aikata bakar fata suna gyara yanayin da suke ciki ba domin ya saba ba, sai dai kawai saboda wani zai iya yi musu wata fassara ta daban, musamman ma idan akwai kyama a kan wadannan masu dabi'ar, wanda hakan kuma zai iya haifar da wata illa.

Wingfield, farfesa a jami'ar Washington da ke St Louis, Missouri, a Amurka ya ce, ''Idan aka dauki dabi'ar ma'aikata bakar fata da sauran tsiraru marassa rinjaye a matsayin bacin rai ko wata damuwa musamman a tsakanin farar fata, to hakan ba karamar matsala zai haifar ba a garesu a wurin aikin da suke.

'Gagarumin aiki'

Wannan hali da ma'aikata bakar fata da sauran tsiraru marassa rinjaye ke samun kansu a ciki a wurin aiki, na zama gagarumin aiki a wurinsu ta yadda suke tashi tsaye haikan domin yin duk yadda za su iya don ganin ba a rika yi musu fassara ta daban ba, wadda ta saba da yadda suke ko halin da suke ciki ko abin da suke nufe da wannan halayya da suka yi. To wannan kan zama gagarumin aiki a wurinsu. Suna aiki suna kuma kokarin kauce wa bayar da wata kafa da abokan aikinsu fafar fata za su iya yi musu wata fassara.

Muddin ba su yi hakan ba, to za a iya samun matsala, wadda ka iya kasancewa ma korarsu daga aiki in ji Ortiz da Mandala.

Duk da haka Ortiz ya bayar da shawarar cewa maimakon a ce an bar nauyi a kan ma'aikata bakar fata da tsiraru marassa rinjaye su rika takura wa kansu wajen kare kansu daga wannan fassara ta daban, to kamata ya yi a ce wuraren aiki sun zama masu rungumar kowa, maimakon a rika nuna wariya ga wasu.

This article was originally produced in English for BBC Worklife.