Abin da ya sa ake kai lalatattun wayoyin ƴan Afirka Turai

    • Marubuci, Daga Ben Morris
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Technology of Business editor

Eric Arthur ba shi da lokacin kansa, a duk ranakun karshen mako yake zuwa tattara lalatattun wayoyin salula a kasar Ghana.

Cikin mako guda, yana tafiyar kilomita sama da 160 daga gidansa da ke Cape Coast, zuwa kantuna daban-daban na gyaran wayar salula, da sauran wuraren da suke da wayoyin da suka lalace.

Idan dawa ta yi kyau, yakan samu lalatattun wayoyin guda 400. Baya ga haka, yana da mutum 6 da suke aiki tare wadanda ke sassa daban-daban na Ghana, kuma a tsakaninsu suna sa ran samun wayoyi 30,000 a shekara guda.

Mista Arthur da abokan huldar suna biyan kudi kalilan wajen sayar kowacce lalatacciyar waya kan kasa da Cidi 3 na kudin kasar.

Duk da cewa wasu daga ciki sun lalace ta yadda ba za a iya gyarawa ba, sai an yi ciniki sosai kafin a daidaita.

"Sabuwar wayar komai-da-ruwanka tana kai wa dala150, ni kuma nakan taya lalatacciyar a kan dala 1. Duk da sun san cewa babu amfanin da za ta yi musu, amma sai su ce ai kaza na saye ta, ta yaya zan sayar da ita da arha haka?'"

Wani kamfanin Holland da ake kira Closing the Loop ne yake biyan shi ladan aikin da yake yi. Kamfanin yana safarar lalatattun wayoyin da su Eric suka tara zuwa kasashen Turai, inda suka sake sabunta su. Sai kuma wani kamfanin na daban ya kwashi kashi 90 cikin kayan da aka yi wayoyin da su, musamman na roba zuwa wasu abubuwan na daban.

Me ya sa safarar wayoyin daga yammacin Afirka?

Joost de Kluijver, wanda ya samar da kamfanin Closing the Loop tare da Reinhardt Smit, ya ce amsar me suka ce har yanzu Afirka ba ta da kamfanin da yake narkar da irin wadannan kayayyakin tare da sabunta su ko yin wani abu na daban, misali suke yin wayar salula.

"Duk wani abu da kake bukata domin yin wannan aikin babu shi," in ji shi. "Babu dokoki, babu ababen more rayuwa da wayar da kai ga masu saya. Kan hakan, ba ka da kudin da za ka zuba wajen tattaro kayayyakin nan da kuma suke sabuntawa."

A bangare guda kuma, ana sayar da wayoyi miliyan 230 a Afirka a kowacce shekara. Idan ba a bukatarsu kamfanonin da suke bukata ke tattaro su, a wasu lokutan kuma zubar da su ake yi.

Kamar yadda Global E-waste Monitor, mai sa ido a duniya, a shekarar 2019 kadai Afirka na samar da kusan tan miliyan 3 na lalatattun kayan latironi, wadanda kashi 1 ne kadai aka tattaro da kuma sabunta.

"Kasashen Afirka sun kware wajen kara wa'adin sabunta kaya. Akwai aikin a kasa, amma yadda za a yi da su shi ne babbar matsalar, musamman wadanda aka daina amfani da su," in ji Mista de Kluijver.

Domin biyan kudin lalatattun wayoyin salula, kamfanin Closing the Loop ya kulla hulda da yarjejeniya da kamfanoni da kungiyoyi, wanda kamfanin ke biyan sama da fam 4 kan kowacce sabuwar waya ga duk wanda ya samar da fasaharta.

Kudin da ake sayen wayar, a ciki ne na dakonta, da karbowa, har da sabuntawa a Afirka, ciki har da ribar da Closing the Loop zai samu.

Mista de Kluijver, ya damu kan shirin samar da kamfanin sabunta kayayyaki a Afirka. Ya ce matukar babu kudaden da za su taimakawa fannin, da kokarin yin doka za su sha matukar wuya wajen ganin abubuwa sun daidaita.

Simone Andersson, na sane da fadi tashin da ake yi kan hakan. Ita ce shugaban fannin kasuwanci na kamfanin Waste Electrical and Electronic Equipment Centre (WEEE) da ke sabunta kayan laturoni a kasr Kenya.

Kenya ba ta da kamfanin da yake yin hakan na gwamnati, amma akwai wuraren da ake tattara kayan da aka yi amfani da su ko lalatattu. Da fari kamfanin WEEE ya fara da musayar na'ura mai kwakwalwa ta makarantu.

Lokacin da suke aiki da makarantun ne suka gane akwai bukatar fara kwashe kayan lataronin da suka lalace da kuma ba a bukatarsu, a shekarar 2012, aka kaddamar da kamfanin sabunta kayayyakin.

A wannan shekarar, cibiyar WEEE na sa ran samun tan 250 na kayan lataroni da suka lalace, yawanci ta hannun abokan huldarsu kamar kamfanin Total Energies da Absa.

Wannan shi ne mafi kankanta cikin tan 50,000, na lalatattun kayan a Kenya a kowacce shekara. Mis Andersson na da burin samar da wurin da za ta kaf yadda za a dinga zuwa ana tara kayan lataronin da ba a amfani da su da wadanda suka lalace ba za a iya gyarawa ba.

Ta kara da cewa 'yan Kenya sun kar sanin illar da tarkacen kayan da ba a amfani da su ke yi wa muhalli, kuma a shirye suke domin yin wani abu domin kare hakan.

"Yawancin mutane sun san matsalolin da wadannan tarkace ke janyowa muhalli. Da yawa daga ciki na son sauya yadda suke tafiyar da lamuransu, inda akwai ababen more rayuwa da ke taimaka musu da tuni an magance wani bangare na matsalar tare da amfani da sake sabunta abun da muke ganin ba shi da amfani ," in ji ta.

Gwamnatin Kenya na son daukar matakan taimakawa, tana wani shiri na samar da wata doka da ta shafi masu samar da kayan, wadda za ta dauki nauyin hidimar sabunta kayan, da sake jigilarsu ga wadanda za su sara domin sayarwa.

"Muna kokarin ganin hakan ta tabbata, saboda muna tsananin bukatar inda za mu dinga sabunta kayan a kasar nan," in ji Mis Andersson. "Muna kuma son ganin Kenya ta zama wadda za ta zaburar da sauran kasashen Afirka don daukar irin matakin.

Burin Mis Andersson shi ne wata rana ta gina ma'aikatar narkar da karafa a Kenya: "Yayin da muke kara bunkasa, tabbas muna bukatar fasahar zamani a Afirka. Mai zai hana a yi a gabashin Afirka? Me ya sa ba za a yi a birnin Nairobi na kasar Kenya ba? Wannan shi ne daya daga cikin burinmu nan gaba."

Idan muka koma can Cape Coast da ke Ghana, Eric Arthur, ya ga gagarumin ci gaba kan yadda ake tafiyar da kwaso tarkacen da suka lalace a 'yan shekarun nan, amma yana ganin ya dace a kara himma.

"Idan aka kara da wayar da kan mutane, na yi amanna za su fahimci bukatar da ake da ita ta sarrafa kayan lataronin da suka lalace ko daina aiki baki daya," in ji shi.

Follow Technology of Business editor Ben Morris on Twitter.