Fafutukar da ake yi don ceto jariran da ke fama da yunwa a Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Elaine Jung da Tom Donkin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Likitoci a asibitocin Afghanistan da ke fama da matsaloli, waɗanda da yawansu a yanzu suna aiki ba tare da biyansu ba, sun bai wa BBC labaran halin tashin hankalin da ƙasar ke ciki da kuma yadda hakan ya sa ba sa iya kula da marassa lafiyarsu ma.
An sauya dukkan sunayen waɗanda aka yi hira da su
Wata matashiya tana kuka, tana roƙon likitan da ya kashe ta ita da ƴarta.
Dr Nuri, wata likitar mata a yankin tsakiyar Afghanistan, tana ƙoƙarin yi wa matar tiyatar haihuwa a lokacin da ta saddaƙar.
'Ban san ta yadda zan iya rayuwa ba,' kamar yadda take faɗa, 'to ta yaya zan iya haifar wani ɗan adam ɗin?'" Matan da suke sashen Dr Nuri suna fama da tamowa ta yadda har sun san cewa da ƙyar su samu ruwan nonon da za su shayar da ƴaƴansu.
Dr Nuri ta ce ɗakunan marasa lafiyan sun cika maƙil ta yadda sai da ta dinga kutsawa ta cikin mata masu naƙuda da ke manne a jikin bangwayen da jini ya ɓata su, wasu kuma suke kwance a kan mayafai masu datti.
Asibitocin da ke kusa da ma na kuɗi masu zaman kansu dole ta sa suka rufe, don haka mutanen da suke zuwa wannan babban asibitin na zamani da ke yankin tsakiyar Afghanistan sun nunka sau uku.
"Sashen masu haihuwa shi ne mafi nutsuwa a kowane asibiti, amma ban da Afghanistan," a cewar likitar matan. Ta ce a cikin mako biyu kawai a watan Satumba ta ga jarirai biyar da yunwa ta kashe su.
"Wajen tamkar lahira yake."
Dama tuni Afghanistan ke fama da tsannain fari da kuma gwamman shekarun da ka shafe ana yaƙi, amma ƙwace ikon da ƙungiyar Taliban ta yi ya sake gaggauta jefa ƙasar cikin durƙushewar tattalin arziki.
Agajin ƙasashen duniya wanda dama shi ne ƙashin bayan tattalin arziki da kuma tsarin kiwon lafiya na gwamman shekaru a ƙasar, da dama ake samun jan ƙafa a kansa, a yanzu ya dakata kwata-kwata a watan Agusta.
Masu bayar da tallafi na ƙasashen yamma sun nnuna babbar damuwa ta aika kuɗaɗe ta hannun gwamnatin da suke ganin ta hana wa mata da yara ƴancinsu, tare da ƙaƙaba tsaurara hukunce-hukunce ga mutane.
Hakan na nufin Afghanistan na fama da yunwa mafi muni a tarihinta, kamar yadda alƙaluman Majalisar Dinkin Duniya suka nuna na baya-bayan nan.
Kusan yara miliyan 14 ne ake tsammanin za su fuskanci tsananin tamowa a wannan hunturun.
A fadin ƙasar kuwa, asibitocin da ke kula da masu fama da yunwar ne suke dab da rushewa, inda tuni aka rufe asibitoci kusan 2,300. Likitoci a yankunan karkara sun ba da bayanan cewa ba sa iya samar da magunguna - ko da kuwa paracetamol ne ga waɗanda suke cikin halin tsananin rashin lafiya, waɗanda suka yi tafiyar awa 12 don neman magani.
A babban birnin ƙasar Kabul, an shiga yanayin da ake samun marasa lafiyar da ta yi tsanani sakamakon yunwa a wani babban asibitin yara.
Daraktan asibitin Dr Siddiqi ya ce an ga ƙaruwar mace-mace a watan Satumba bayan da aka yanke ba da tallafi, inda yara kusa huɗu ƴan ƙasa da shekara 10 ke mutuwa duk sati sakamakon tamowa ko cututtuka masu alaƙa, kamar guba daga abinci mara tsafta.
Ya ce matsalar ta fi shafar ƙaramin cikinsu ne, yayin da ƴan ƙasa da shekara biyar kuma aka gaza ceto su.
"Waɗannan yaran yawanci sukan mutu ne kafin ma a kwantar da su a asibiti... Mun rasa mutane da dama ta hakan," ya ce.
A sashen haihuwa na Dr Nuri kuwa, ana yawan ɗauke wuta wanda hakan ke jawo yawan mace-mace. Jarirai bakwaini da dama sun mutu a cikin kwalaben da ake kula da su sakamakon hakan, a cewarta.
"Akwai matuƙar takaici ka ga suna mutuwa a kan idonka."
Ta kuma ce yawan ɗauke wutar ya sa an samu ƙaruwar mutuwar mutane a yayin da ake musu tiyata.
"Akwai ranar da muke cikin yin tiyata sai aka ɗauke wuta. Sai komai ya tsaya. Sai na ruga da gudu ina ihu. Akwai wani da ke da mai a cikin motarsa sai ya ba mu don mu sa a janareto mu tayar.
Sai ta ce, a kowane lokaci idan ana tiyata a asibitin, "Na kan cewa mutane su yi sauri. Abin akwai ɗaga hankali da yawa."

Asalin hoton, Getty Images
Dr Rahmani, daraktan wani asibiti a gundumar Herat, wanda ya ƙware a kan duba marasa lafiyan da ke fama da cutar korona, ya nuna wa BBC wata wasiƙa da ya samu daga ma'aikatar lafiya ta gwamnatin Taliban, mai kwanan watan 30 ga Oktoba, da aka nemi ma'aikata da su ci gaba da aiki har sai an samu kuɗaɗen tallafi sannan a biya su.
A ranar Talata, Dr Rahamani ya tabbatar da cewa a yanzu an rufe wannan asibitin nasa saboda ba a samu kuɗaɗen ba, kuma hotuna sun nuna yadda ake fitar da marasa lafiya daga asibitin a kan gadajen ɗaukar mara lafiya.
Babu tabbas kan abin da zai faru da su.
A kusa da nan kuma akwai wani asibitin da suka ƙware kan warkar da ƴan ƙwaya wanda shi ma ake fafutukar samar da abubuwan buƙata ga marassa lafiya, waɗanda ba za a iya ci gaba da duba su ba ta hanyar daidata tunaninsu idan babu magani.
"Akwai marasa lafiyan da sai da aka ɗaure su da sasari, da kuma waɗanda aka ɗaure hannayensu da ankwa saboda hare-haren da suke kai wa.
"Muna shan wwahalar kula da su sosai," a cewar Dr Nowruz, daraktan asibitin, yana mai ƙarawa da cewa - idan babu cikakkiyra kulawa - "to asibitin namu zai zame musu tamkar kurkuku."
Amma shi ma wannan asibitin a yanzu ana dab da rufe shi saboda rashin ma'aikata, kuma idan aka rufe shi Dr Nowruz ya damu da abin da ka iya samun marasa lafiyarsa a lokacin hunturun nan.
"Ba su da muhalli. Yawanci suna rayuwa ne a wurare kamar ƙarƙashin gadoji, da kwangaye da maƙabartu, wuraren da suke da wahalar zama ga ƴan adam," ya ce.
Ministan lafiya na gwamnatin Taliban Dr Qalandar Ibad, ya shaida wa sashen BBC Fasha cewa a watan Nuwamba gwamnatinsa na aiki da ƙasashen waje don sake dawo da tallafin da suke bayarwa.
Kazalika, manyan masu ba da tallafi na duba yiwuwar jingine Taliban a gefe, suna tsoron cewa ba lallai a yi amfani da tallafin ta yadda ya dace ba.
A ranar 10 ga watan Nuwamba MDD ta yi nasarar aikata hakan a karon farko - inda ta zuba dala miliyan 15 ga tsarin lafiyar ƙasar.
An yi amfani da kusan dala miliyan takwas don biyan wasu ma'aikatan lafiya 23,500 a watan da ya gabata. Duk da cewa dai kuɗin da aka samu zuwa yanzun ba su taka kara sun karya ba, sauran masu ba da tallafi na ƙasashen duniya na fatan bin sawu wajen bayarwa. Amma dai lokaci na ƙurewa.
"Kwanan nan za mu ji ana cewa ba mu da isasshen ruwan sha," a cewar Dr Nuri, a yayin da marassa lafiya ke ƙoƙarin samun inda za su ji ɗumi a lokacin sanyi.
Tsananin sanyin da ake ciki zai sa kwanan nan a kasa shigar da sauran kayayyakin tallafi cikin ƙasar daga Pakistan da Indiya.
"A duk sanda matan nan suke barin asibitinmu da jariransu, nakan yi ta tunaninsu. Ba su da kuɗi, ba za su iya sayen ko da abinci ba," ta ce. Ita ma a yanzu haka iyalanta na cikin halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi.
"A matsayina na likita ba ni da isasshen abincin da zan ci - ba zan iya saya ba kuma na kashe dukkan wasu kuɗaɗe da na tara.
"Ban ma san me ya sa har yanzu nake zuwa aiki ba. Kullum da safe sai na tambayi kaina wannan. Amma wataƙila saboda har yanzu ina fatan samun kyakkyawar rayuwa ne a nan gaba."
Waɗanda suka taimaka wajen samun ƙarin rahotanni daga Ali Hamedani da Kawoon Khamoosh da Ahmad Khalid da Hafizullah Maroof












