Tsafta: Shin kicin ɗinku ya fi banɗaki yawan ƙwayoyin cuta?

Un homme en gants de nettoyage pose dans sa cuisine

Asalin hoton, Prostock-Studio

Kimanin mutane miliyan 2 da dubu ɗari 4 na kamuwa da cutar guba a abinci a kowace shekara a Burtaniya, a cewar Hukumar Kula da Ingancin Abinci.

Yayin da gidajen abinci da kantunan sayi-ka-tafi ke da alhakin yawancin matsalar, sauran na tattare ne a dakunan abinci na cikin gida.

Wasu ƙwayoyin cutar ku da kanku kuke sa su a abinci lokacin da kuke girki.

Shin kuna wanke hannuwanku lokacin da kuka koma gida da kafin dafa abinci?

Yaushe rabonku da tsabtace wayarku - musamman ma idan kuna amfani da ita wajen koyo ko yin girke-girke? Shin kun san ko mayanin goge kwanukanku na abinci yana da tsafta?

Ƙwayar cutar Norovirus, wadda ke sa amai a lokacin hunturu, ita ce mafi yawan nau'in guba a abinci.

To amma sauran ƙananan ƙwayoyi ma na bakteriya da bairus da ire-irensu su ma suna sa mu rashin lafiya.

Ya iya kasancewa kuna da tarin tambayoyi a game da ƙwayoyin cuta, domin akwai ƙwayoyin bakteriya a kan katakon yanke-yankenku na girki (za mu yi magana kan wannan a gaba).

To a nan za mu duba hanyoyi da dama da ƙwayoyin cuta ke shiga cikin bakinku, tare da taimakon likitar tsafta, Dr Lisa Ackerley.

Akwai dubban ƙwayoyin cuta a hannunka

Un téléphone photographié dans une toilette

Asalin hoton, NA

Yawanci cututtuka masu yaduwa suna bazuwa ne ta hanyar taɓawa. Tun da hannayenku suna ɗauke da ƙwayoyin cuta kusan 3,000 na nau'ikan sama da 150 (yawancinsu ba su da lahani) a lokaci guda, to ku yi tunanin yawan ƙwayoyin cutar da za ku iya shigarwa wajen dafa abincinku idan kuna girki ba tare da wanke hannunku ba.

Daɗin daɗawa ma, ƙwayoyin cuta suna yaɗuwa daga baki da hancinku zuwa hannayenku.

Wanke hannuwanku ta hanyar da ta dace yana taimakawa kawar da waɗannan cututtukan.

Wanke hannu da ruwa kawai yana rage yawan ƙwayoyin cuta da kashi 23 cikin dari , amma wanke hannu da sabulu da ruwa na iya rage yawan zuwa kashi 8 cikin dari, a cewar wani bincike.

Sai dai fa duk da haka ba wai kuna kashe ƙwayoyin cutar ba ne, kuna kawar da su ne kawai.

Wannan ne ya sa dole ku riƙa tsaftace wurin wanke-wankenku!

Dr Ackerley ta ce: "Lokacin da kuka koma gida ku wanke hannayenku. Idan kuka je aiki ku rika wanke hannayenku. Ba ku san abin da kuka ɗauka a hanya ba. Wadannan muhimmin lokuta ne."Wannan shi ne ya sa ko da ruwan sanyi ko na zafi kuka yi amfani wajen wanke hannuwan ba wani bambanci.

Ɗaya daga cikin wayoyin hannu shida na dauke da kwayoyin cuta na kashi

Wataƙila kuna tare da wayarku a ko'ina hatta a bandaki. Wani bincike da kungiyar wayar da kai kan amfanin wanke hannu ta Birtaniya (UK Global Handwashing Coalition) ta sa aka yi ya nuna cewa, a duk wayar hannu shida ana samun daya mai dauke da kwayoyin cuta na kashi.

Kimanin kashi 57 cikin dari na 'yan Birtaniya suna amfani da wayoyinsu a bayan gida, in ji kamfanin YouGov da ke gudanar da bincike. Ba mamaki ashe da yawancin wayoyi ke dauke da tarin ƙwayoyin cuta na kashi.

Ire -iren wadannan kwayoyin cuta na iya rayuwa a hannaye da kan abubuwa har tsawon sa'o'i, musamman idan jikin abin ko wurin na da zafi kuma ba ya fuskantar hasken rana kai tsaye, kamar wayar da ta yi zafi a aljihunka.

Daga nan, wasu mutanen na iya ɗaukar ƙwayoyin cuta ko kuma su yada su ga wasu abubuwan kamar abinci ko hannun ƙofa ko hannun tukunya.

"Idan kuna amfani da wayarku sosai hannunku da datti, to ya kamata ku tabbatar kun goge ta kuma ku wanke hannuwan naku kafin ku fara dafa abinci," in ji Dr Ackerley.

Ta kuma yi gargadi kan hadarin yada kwayoyin cuta na bakteriya daga abinci zuwa jikin wayar salula: "Idan kun taba danyen nama, ku wanke hannayenku kafin ku taba wayarku."

Une main qui nettoie le plan de travail

Asalin hoton, Charday Penn

Kashi 60 cikin ɗari na mayanin goge kwanuka na gurɓace da ƙwayoyin cuta na E. Coli

Yayin da kashi 60 cikin ɗari na mayanin goge kwanuku ke gurbace da ƙwayar cutar e. coli, a cewar wani bincike da Kungiyar Masana Harkokin Tsafta ta Duniya, haka su ma sauran mayanai da ake amfani da su a ɗakin dafa abinci suna ɗauke da tarin ƙwayoyin cuta, to me za ku iya yi domin rage yaduwar ƙwayoyin cuta?

"Mutane da yawa suna amfani da mayanin goge kwanuka barkatai. A iya cewa wataƙila su ne mafiya ƙazanta a abubuwan da ke ɗakin dafa abinci.

Kuna ɗibar ƙwayoyin cuta yayin da kuke goge kwanuka da sauran abubuwa akwai kuma lokacin da za ku sanya datti a kan wurare ko abubuwa," in ji Dr Ackerley.

Ga wasu hanyoyi na tsaftace mayani:

A riƙa amfani da mayani daban-daban wajen goge kwanuka da dabe da goge hannu da sauran wurare ko abubuwa.

A riƙa wanke mayani da ruwa mai dumi da ya kai zafin sama da 60 ° C (mafi dacewa sama da 80 ° C).

Idan na'urarku ta wanke ko tsaftce kwanuka ba ta amfani da ruwa to sai ku sanya mayanan a wani kwano da ruwa da garin sabulu ku tafasa.

Famfunan banɗaki sun fi teburin wurin dafa abinci tsabta

Wani bincike na 2011 ya gano cewa kashi 32 cikin ɗari na kantar ɗakin dafa abinci na ɗauke da ƙwayoyin cutar bakteriya cikin har da wadda ake samu a cikin kashi.

A wanan bincike dai an gano cewa kashi 9 cikin ɗari ne kawai na wurin kunna fanfunan banɗaki ke dauke da kwayoyin cutar.

Ƴan mitsi-mitsin halittu da ba a iya gani da ido za su iya rayuwa ne daga tsakanin ƴan sa'o'i zuwa kwanaki, abin dai ya dogara ne ga yanay8insu da kuma inda aka same su.

To amma ya kamata a ce mu duka mun nemi maganin kashe ƙwayoyin cuta?

A 2018, shirin BBC na Trust Me I'm a Doctor ya gano cewa wani dan tsinke mai auduga naɗe a jikinsa da aka ɗauko daga kan teburin ɗakin dafa abinci na wani gida, bayan sa'a ɗaya da goge teburin sosai, yana ɗauke da ƙwayoyin cuta na bakteriya. Kuma bayan sa'o'i 12 sai aka ga yawan ƙwayoyin cutar ya yi ƙaruwa ta ban mamaki.

A wata maƙala da ya rubuta ta BBC, Dakta Michael Mosley ya yi bayanin cewa: "Idan kuka yi amfani da maganin kashe ƙwayoyin cuta na bakteriya domin kariya daga garesu, zai iya kasancewa ka yi asarar lokaci da kuɗinka.

Domin ba kawai za su sake girma su dawo ba kaɗai za su yi hakan ne ma cikin sauri, to amma yawancin irin waɗannan ƙwayoyin da ke zaune a gidajensu ba masu cutarwa ba ne, hasali wasu ma suna da amfani ga lafiyarmu.''

Duk duk da haka, Dakta Ackerley ya yi amanna cewa abu ne mai muhimmanci a yi amfani da maganin kashe ƙwayoyin cuta a tsaftace wuraren aikin a muhimman lokuta, kamar lokacin da aka sarrafa ɗanyen nama ko kifi.

Un couteau sur une planche à couper

Asalin hoton, NA

"Dole ne ka yi amfani da maganin kashe ƙwayoyin cuta a wuraren da nama ko kifin ya taɓa domin kada kabar wa wanda zai zo daga baya ya yi amafani da ɗakin dafa abincin wata ƴar tsaraba.''

Akwai ƙwayoyin cuta a kan katakon yanke-yankenku na girki fiye da kan salgarku (ta tangaran).

"Yawanci ana samun ƙwayoyin cuta na bakteriya na kashi kusan ninki 200 fiye da yadda ake samu a kan salgar da ake zama (ta tangaran)," Kamar yadda Dakta Chuck Gerba, farfesa a fannin nazarin ƴan mitsi-mitsin halittu (microbiology) a Jami'ar Arizona, ya gaya wa BBC.

Ba wai lalle ba ne ana samunsu ta hanyar haɗuwa da kashi, sai dai ta ɗanyen nama.

Idan za a wanke kayan ɗakin girki ne da aka sarrafa nama, "na'urar wanke-wanken kwanaku ko tangaran ita ce ta fi amfani," in ji Dakta Ackerley.

Idan ba ka da ita to akwai hanya biyu da za ka tsaftace katakon yanke-yankenka na ɗakin girki: da ruwan magani ko kuma gashi.

Idan za ka wanke katakon yanke-yanken naka, sai ka sanya shi a wurin wanke-wanke ka zuwa mishi maganin kashe cutukan, sai ka bar shi zuwa wani ɗan lokaci kafin ka wanke shi.

Haka kuma za ka iya zuba masa ruwan zafi a hankali domin ka kashe ƙwayoyin cutar na bakteriya. Idan ka goge katakonka ba tare da ka wanke shi da maganin kashe ƙwayoyin cuta ko ruwan zafi ba, to kana fuskantar haɗarin yaɗa ƙwayoyin cuta ga mayani ko burushinka.

Ya fi dacewa ka ware wuƙa da katakon yanke-yankenka na sarrafa kifi da dama, wani kuma ka ware shi domin wasu abubuwan.

Wajen wanke-wankenka na ɗakin girki yana damunka da wari?

Zai iya kasancewa akwai miliyoyin ƙwayoyin cuta a bututun wurin, to amma ta hanya da kuma yadda suke shiga jikinka ne babban abin damuwa, in ji Dakta Ackerley.

Main gantée d'un nettoyeur qui lève le pouce sur fond jaune

Asalin hoton, NA

Yawanci mukan wanke hannuwanmu a wurin wanke-wanke na dakin abinci , to amma ta hakan za ka iya sanya datti a wurin in ji ta. Saboda haka duk abin da ka sa za ka wanke shi a wurin wadannan kwayoyin cuta za su iya kama shi.

To hanyar kauce wa gurbata kayan abincinka ko kwanuka ko kofi da wadannan kwayoyin cuta, ita ce ka wanke su a gefe a famfo, maimakon ka zuba su a wannan wuri na wanke-wanke da ake tara ruwa ka wanke, in ji Dr Ackerley.

Akwai kwayoyin cuta (e. coli) a firjinku?

Babban amfanin firji shi ne, ya jinkirta girman kwayoyin cuta tare da tsawaita lokacin da abinci zai kai bai lalace ba.

To amma idan har aka ce kwayar cuta ta riga ta hau abincin kuma ta girma, matsala ta zo, domin ana gano cewa ita kanta kwayar cuta ana samunta a cikin firji sandiyar hakan, kuma ta rayu har tsawon makonni.

Saboda haka akwai bukatar a rika tsaftace firji damaganin kashe kwayoyin cuta.

Doka ta uku?

Shin ya dace a ci abincin da ya fadi ko da dakika uku kawai ya yi a kasa?

Idan abu ne da za a bare kamar tuffa ko lemo ko kuma za a dafa to wannan ba matsala.

Amma idan ba irin wadannan ba ne, misali a ce wani kosai ko burodi ko nama ko kifi da makamantansu, to bai dace ba ko da kuwa dakika nawa suka yi a kasa ko da faduwarsu aka yi sauri aka dauke, saboda zai iya kasancewa ya rigaya ya gurbata da kwayoyin cuta.

Hanyoyi uku na kariya daga kwayoyin cuta

Ba sai an shafe duk tsawon lokaci ana ta kokarin tsaftce dakin dafawa ko hada abinci ba.

Abin da kamata kawai shi ne;

Muhimmin abu a nan shi ne a kiyaye da matakan tsafta, kamar wanke hannu yadda ya dace kuma a lokacin da ya kamata.

Tsaftace wuraren da aka san an dora wani abu kamar danyen nama ko kifi ko wani abu da zai iya yada kwayoyin cuta, bayan an kammala aiki.

A tanadi kayan goge-goge da tsafta, kamar a ware tsumma ko mayanin goge abubuwa daban-daba a dakin dafa abinci.

Haka kuma yana da kyau a guji cin abincin da ya dade a kasa !