Muhammadu Sanusi II: Abu biyar kan taron cikar tsohon Sarkin Kano shekara 60 a duniya

A ranar Asabar ne aka gudanar da taron gabatar da makaloli na shekara-shekara kan cikar tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II shekara 60 a duniya.
An gudanar da taron ne a dakin taro Umaru Musa 'Yar Adua da ke birnin Kaduna a jihar ta Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.
Taron shi ne irinsa na farko kuma ana sa ran za a ringa gudanar da shi a kowace shekara.
A wajen taron, masana sun gabatar da makaloli kan irin sauye-sauyen da Sarki Sanusi ya kawo a wuraren da ya samu damar yin aiki.
Yusuf Ibrahim Yakasai ya halarci taron, ya kuma duba abubuwa biyar daga cikin muhimman abubuwan da suka dauki hankali a taron.
Me sarki Sanusi ya ce?
A jawabinsa, Malam Muhammadu Sanusi ya ce idan ya yi waiwaye ya dubi shekaru 60 da ya yi a duniya, yana shiga halin damuwa da kunci, saboda yadda aka samu koma-baya a bangarorin rayuwar Najeriya.
Sarki Sanusi ya ce Allah ya yi masa baiwar da ba wani dan Najeriya da ya taki irin sa'ar da ya samu.
Ya ce ya zama Shugaban bankin kasuwanci, daga nan ya zama gwamnan babban bankin Najeriya, ya zama Sarkin Kano, sannan yanzu ya zama Khalifan Tijjaniyya.
"Babu wani dan Najeriya da ya samu irin wadannan damarmaki da na samu," in ji tsohon Sarkin Kano na 14.
"Dukkan wani shugaba na kasar nan ko duk wani shugaba na arewa a wannan lokacin bai kamata ya zauna cikin farin ciki ba saboda halin da mutanenmu suke ciki.
"Ko kai kana cikin tsaro, al'umma ba sa cikin tsaro. In kai ba ka cikin yunwa, al'umma na cikin yunwa. Kuma mutanen nan su ne mu."
A cewar Sarki Sanusi kullum aka tuna halin da suke ciki dole ya zama ba a ji dadi ba.
"Don amanar da Allah ya dora mana ba za a mu iya dauka ba.
Dangane da tattalin arziki kuwa, Sarki Sanusi ya ce duk matsalolin da Najeriya ke ciki a yau suna da dangantaka da matsalar tattalin arziki.
Ya ce matsaloli da suka hada da satar mutane don neman kudin fansa, da rikicin makiyaya da manoma da ta'addanci, da shaye-shaye da barace-barace duk suna da dangantaka mai karfi da tattalin arziki.
"Duk inda ka duba me yake kawo garkuwa da mutane? Me yake kawo fashi da makami? Me yake kawo rikici tsakanin makiyaya da manoma?
"Duk rigima ce kan tattalin arzikin kasa da halin rayuwa" in ji Khalifan na Tijjaniyya.
Ya kara da cewa bai taba nadama kan duk wani mataki da ya dauka ba, kuma dama yana sane da cewa akwai abin da zai iya bayan duk wani mataki da ya dauka.
Ya ce ba ya tsoron bayyana duk wani ra'ayi da ya yi amanna cewa shi ne ra'ayi na gaskiya.
Babe ne mai karfin gaba - Sarkin Zazzau

A tattaunawarsa da BBC bayan kammala taron, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya ce duk wajen da Muhammadu Sanusi ya samu kansa sai ya bar wani kyakkyawan abin yabo.
Sarkin Zazzau ya ce Khalifan na Tijjaniyya mutum ne da ba ya shakkar duk wani abu da zai iya faruwa da shi. Don haka babe ne mai karfi gaba," in ji Sarkin Zazzau.
Shi ne Sarkin Kano na farko da ba shi da ƙwarƙwara.
Daya daga mutanen da suka gabatar da makaloli a wajen taron, wani mai bincike kuma marubuci, Malam Ibrahim Ado Kurawa ya ce, Sarki Sanusi ya kawo wasu sauye-sauye guda hudu lokacin da yake Sarkin Kano.
"Na ɗaya ya ɗara danƙon zumunci tsakanin zuriyar Dabo, wato sarki na biyu a jerin sarakuna Fulani," in ji shi.
Ibrahim Kurawa ya ce akwai gidajen sarauta da suka shafe fiye da shekaru 50 ba su da wani mukami, amma a zuwan Sarki Sanusi duk ya janyo su ya ba su mukamai.
Na biyu, a cewar Malam Ibrahim Kurawa shi ne, gyara gidan Sarkin Kano.
Ya ce tun bayan gina fadar ta Sarkin Kano shekara 500 da suka gabata, babu wani sarki da ya gyara gidan yadda zai tafi da zamani kamar aikin da Muhammadu Sanusi ya yi.
Abu na uku a cewar marubucin shi ne matakin da ya dauka na samar da wani kundi kan dokokin zamantakewa.
Na hudu shi ne kasancewar Sarki Muhammadu Sanusi II Sarkin Kano na farko da ba shi da kwarkwara.
Ya ce bayan zamansa sarki, ya rushe tsarin kwarkwara, sannan ya sa aka mika duk ayyukan Uwar Soro (wacce ita ce shugabar kwarkwarori) ga Giwar Sarki, wato matarsa ta fari Hajiya Sadiya Ado Bayero.
Ya gagari duk yan majalisar wakilai
Wani abu da ya dauki hankalin mahalarta taron shi ne jawabin Farfesa Kingsley Moghalu, wanda ya yi aiki da Muhammadu Sanusi a matsyin mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya.
Farfesa Moghalu ya ce a lokacin da suke aiki Sarki Sanusi ya taba tsayawa gaban 'yan majalisar wakilan Najeriya da niyyar yi masa titsiye a kan wata magana da ya yi.
Amma a cewar Kingsley kafin Muhammadu Sanusi ya gama bayani sai da ya gamsar da yan majalisar da ma duka 'yan Najeriya cewa ya fi 'yan majalisar gaskiya.
An gabatar da bayani ta manhajar zoom
Duk da cewa an gudanar da taron ne a dakin taro na Umaru Musa Yar Adua da ke dandalin Murtala Square a Kaduna, wasu daga suka gabatar da jawabai sun gudanar da su ne kai tsaye daga wani wajen da suke ta amfani da manhajar Zoom.
Babban mai gabatar da jawabi Farfesa Andrea Brigaglia ya gabatar da tasa makalar ne daga kasar Italiya ta manhajar Zoom.
Andrea Farfesa ne kan nahiyar Afirka da Asiya da yankin meditareniya a Jami'ar Napels L'Orientale a Italiya.
Haka shi ne babban limamin masallacin Alfurkan a Kano, Dakta Bashir Aliyu Umar ya gabatar da tasa makalar daga Kano ta amfani da manhajar Zoom.
Shi kuma gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-rufai ya turo da sakon bidiyo ne na fatan alkhairi ga taron, kasancewar baya Najeriya a lokacin.
Mahalarta taron

Daga cikin wadandan suka halarci taron akwai Mai Martaba Sarkin Ringim Alhaji Sayyadi Abubakar, wanda kaka yake ga Sarki Sanusi II, da gwamnan jihar Sokoto Aminu Wazirin Tambwal.
Akwai mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna Hajiya Hadiza Balarabe da Sarkin Awe, wanda ya zama mai masaukin Muhammadu Sanusi II, lokacin da aka sauke shi daga Sarauta aka kuma kai shi jihar Nasarawa.
Malam Ibrahim Sanyi-Sanyi shi ne shugaban kwamitin shirya taron, ya ce sun shirye taron ne ganin cewa rayuwar Khalifan na Tijjaniyya cike take da darasi musamman ga matasa.











