Masu rajin kafa dimokaraɗiyya, masu kama-karya da masu neman karɓe iko a Tunisia

Magoya bayan shugaban ƙasa sun goyi bayan matakin

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan shugaban ƙasa sun goyi bayan matakin
    • Marubuci, Daga Magdi Abdelhadi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai sharhi kan Arewacin Afirka

Idon duniya ya koma kan kan ƙaramar ƙasar da ke Arewacin Afirka da aka fara juyin juya hali a Gabas ta Tsakiya a 2011 wanda ya kai ga hamɓarar shugaban mulkin kama -karya wanda ya shafe shekaru 27 yana mulki.

Juyin juya halin da aka ƙaddamar a Tunisia ya girgiza ƙasashen Larabawa kuma har yanzu babu wanda ya san lokacin da za a farfaɗo daga tasirinsa kan makomar yankin.

Wannan ƙalubalen ya ƙara tabbata bayan 25 ga Yuli lokacin da shugaban gwamnatin boko zalla Saied ya ba duniya mamaki bayan sanar da dakatar da majalisa da rusa majalisar zartawa wanda ke nuna wata babbar barazana ga ƙasar Tunisia.

Waɗannan karfin matakan iko ya kamata wa'adinsa kada ya zarta kwana 30. Amma babu tabbas ko zai tsawaita wa'adin na ƙarfin ikonsa, ko kuma zai bijiro da wani abu daban.

Fatan samun jajirtaccen shugaba

Taɓarɓarewar tattalin arziki (ya taɓarɓare da kashi 8 a bara), ƙaruwar rashin ayyukan yi (da kashi 17) da kuma wani ɓangare na ƴan siyasa da ke yaɗa manufa ga ƴan Tunisia cewa tsarin mulkin dimokuraɗiyya bai dace da ƙasar ba.

An baza jami'an tsaro a harabar majalisa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An baza jami'an tsaro a harabar majalisa

Bugu da ƙari ga tasirin annobar korona. Tunisia ta fi yawan masu kamuwa da cutar a Afirka.

Duk wannan ya ƙara haifar da rashin tabbas a tsakanin ɗimbin ƴan Tunisiya kan imani da majalisar dokoki da jam'iyyun siyasar ƙasar.

Wannan ya sa matakin da Mista Saied ya ɗauka ya samu ƙarbuwa daga ƴan ƙasar waɗanda suka fito saman titi suna murna.

Magoya bayansa sun gaji da majalisa, don haka suke neman wani jajirtaccen shugaban da zai saisaita ƙasar.

Amma ko Mista Saied zai iya?

"Fatan samun tsayayyen shugaba ba shi ne maganin matsalolin Tunisia ba," kamar yadda wata mujallar tattalin arziki ta yi gargaɗi a sharhin editanta.

Murnar masu mulki

Haka ne ba kowa ke murna ba a Tunisia ba. Babba a cikinsu Ennahda, jam'iyyar ƴan uwa musulmi da ke da ƙarfi a majalisa.

Ta yi Allah wadai matakin Mista Saied wanda ta kira juyin mulki. Haka kuma sauran jam'iyyun siyasa da masu sa ido sun goyi baya.

Magoya bayan Ennahdha sun yi zargi shugaban da yin juyin mulki

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan Ennahdha sun yi zargi shugaban da yin juyin mulki

Shugabannin yankin kuma daga Masar zuwa tekun Fasha sun nuna goyon bayansu ga matakin Mista Saied. Masu da'awar dimokuraɗiyya kuma sun bayyana fargaba.

Sashe na 80 na kundin tsarin mulki, wanda Mista Saied ya kafa hujja da shi, ya ba shi ƴancin ɗaukar mataki cikin wani yanayi na musamman.

Amma babu inda ya ce yana da ƴancin dakatar da majalisa da janye rigar kariya ga ƴan majalisa da kuma rusa majalisar zartarwa.

Hakan ya sa wasu da dama bayyana matakin da Mista Saied ya ɗauka a matsayin "juyin mulki".

Mista Saied ba shugaban mulkin soja ba ne, an zaɓe shi ne a zaɓen 2019.

Ra'ayi ya bambanta tsakanin waɗanda ke dogaro da kundin tsarin mulki, da kuma waɗanda suke ganin mutane ne suka fi muhimmanci.

Shugaba Kais Saied ya lashe zabe da kashi 70 na kuri'a

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Shugaba Kais Saied ya lashe zabe da kashi 70 na kuri'a

A yanzu, Mista Saied yana da goyon bayan mutane kan titi.

Amma babu wanda ke musanta wannan wani mataki ne da zai iya kawo ƙarshen tsarin gwamnatin Tunisia da ta ƙunshi kowa.

Masu sharhi da dama sun bayar da misali da abin da ya faru a Masar a 2013, lokacin da Abdul Fattah al-Sisi ministan tsaro a lokacin, ya tsige shugaban da aka zaɓa na jam'iyyar ƴan uwa musulmi, murnar da aka yi a lokacin ya yi kama da abin da ya faru bayan sanarwar da Mista Saied ya yi a Tunisia.

Amma akwai muhimman bambanci.

Mista Saied an zaɓe shi inda ya samu kashi 70 na ƙuri'u, kuma sojoji ba su taka wata rawa ba a siyasar Tunisia, amma a Masar sun yi tasiri a ƙasar tsawon shekara 70.

Tunisia saɓanin Masar, tana da ƙungiyoyin ƙwadago mai ƙarfi da kuma ƙungiyoyin farar hula.

Gwamnatoci 10 a shekara 10

Ido ba zai koma kan Mista Saied kawai ba, amma ga sauran hukumomi huɗu - da ke yin tattaunawar ƙasa - inda a 2013 aka cimma matsaya tsakanin masu ra'ayin islama da ƴan boko zalla wanda ya kawo ƙarshen rikici.

Korona ta yi tasiri ga koma bayan yawon bude ido a Tunisia

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Korona ta yi tasiri ga koma bayan yawon bude ido a Tunisia

Wannan ya sa suka samu lambar yabo ta Nobel a 2015.

Akwai kiran da ake yi na taron ƙasa. Amma yana da wahala a iya tunanin komawa kafin sauye-sauyen da ya jefa Tunisia cikin rikici.

Wasu na ganin matsalar ta dogara ne da kundin tsarin mulki wanda ya bayar da damar tsarin shugaban ƙasa da firaminista da majalisa.

A tsarin da ke ba diba ayyukan ɓangarorin gwamnati da ke hana shugaban ƙasa mamaye shugabanci.

Kuma ko dokokin zaɓe sun taimaka ga hura rikicin, wanda ya ba ƙananan jam'iyyu kujerun majalisa.

Saboda wannan, Tunisia ta yi gwamnatoci 10 a shekaru 10.

Yayin da rikicin ke ƙaruwa, musamman kasa shawo cutar korona - tsarin ya lalace, inda shugaban ƙasa da majalisa suka dinga caccakar juna, kuma ɓangarorin biyu suka dinga wallafa ɓangaren doka da ya yi masu ɗadi a Twitter.

Abin da ya faru a Tunisia ba zai tabbata ba, kamar yadda tarihi ya nuna.