Dacewar kwayar halitta: Binciken kimiyya ya tabbatar da batun cewa soyayya gamon jini ce

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Rebecca Thorn
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Bisa al'ada soyayya ba tana somawa ne ta hanyar kawo mutane biyu da ba su san juna ba su tofa yawu cikin bututun binciken kimiyya.
Amma a wajen Cheiko Mitsui, musayar yawu ya ba ta amsar da ta jima tana nema. Ta yi dacen masoyi kuma ta shirya zama matarsa.
Yin amfani da kwayoyin halitta na DNA domin hada soyayya tsakanin mutane abu ne da ke daukar hankalin jama'a.
Sai dai dacewar ƙwayar halitta na samun karbuwa a duniya. Shafukan intanet da dama suna bai wa samari da yan mata irinsu Cheiko kafar kulla soyayya mai armashi yayin da ake bai wa ma'aurata damar yin gwajin dacewar kwayar halitta.
Muna magana da mutane ta hanyar amfani da kwayoyin halittarsu da sunan soyayya domin ganin ko kimiyya na da wajen zama a lamuran da suka shafi soyayya.
'Muhimmin sauyin rayuwa'

Asalin hoton, Cheiko Mitsui
Cheiko Mitsui ta dade tana neman wanda zuciyarta take so kusan shekara 10 ke nan a lokacin da ta gano tsarin hada soyayya ta kwayar halitta.
Auren Mitsui mai shekara 45 daga birnin Hakodate da ke Hokkaido a Japan ya mutu tana shekara 35 har ma ta fara yanke kauna daga samun dacewar rabin rai.
"Na hadu da mutane ta hanyar kawayena a wuraren liyafa sannan na shiga wata hukuma ta hada aure amma duk ban dace da masoyin da ya dace da ni ba," in ji ta.
An hada Mrs Mitsui da wata mai kulla soyayya Cheiko Date wadda take ikirarin kulla soyayya tsakanin ma'aurata 700 cikin shekara 20 da ta shafe tana sana'ar.
A 2014 ta fara aiki da wani kamfanin Switzeeland GenePartner wanda yake ikirarin gwajin kwayar halitta na iya zama wani abin ƙari ga masu dalilin aure.
"Yana da mahimmanci a samu bangarori biyu: daya na dacewar kwayar halitta ko gamon jini," in ji Dr Tamara Brown, daya daga cikin wadanda suka kirkiri GenePartner. "Daya bangaren shi ne taku ta zo daya. Sannan duka wadan nan abu biyu akwai bukatar su zo dai-dai domin samun dacewar soyayya."
Dr Brown ya ce GenePartner ya yi gwajin kan ma'aurata 250 kuma ya gano irin tsarin.
"Idan ka hadu da mutum, ba wai kamanni bane, wani abu ne na daban sannan idan mutum ya yi maka, toh an dace.

Asalin hoton, Cheiko Mitsui
Cheiko Mitsui ta ce tana fatan binciken kwayar halitta zai sa hankalinta ya kwanta wajen zabin wanda za su sha soyayya mai dorewa.
A Satumbar 2018, an hada ta da Tomohito mai shekara 45 duba da irin wasu abubuwansu da suka zo daya. Bayan wata daya suna soyayya ne suka yanke shawarar lokaci ya yi su yi binciken dacewar kwayar halittarsu.
"Sakamakon binciken bai zama dari bisa dari ba amma kuma an kusa dacewa," in ji Mrs Mitsui. "Na sa ran ganin kyakkyawan sakamako amma ya zarce abin da na yi tunanin gani, kuma na yi murna."
Mitsui ta ce mako biyu bayan nan suka yanke shawarar yin aure saboda binciken kwayar halittar tasu ya kwanta musu a rai.
Sun yi aure a Satumbar 2019, shekara daya bayan sun hadu. Mrs Mitsui ta ce tana ji a ranta ta dace saboda kwarin gwiwar da suka samu daga binciken.
"Ban sani ba ko zan iya auransa ba tare da yin gwajin kwayar halittar ba," in ji ta. "Watakila da na yi hakan, amma gaskiya binciken ya kara bani kwarin gwiwar aurensa.

Asalin hoton, Cheiko Mitsui
Sai dai Dr Diogo Meyer, wani masanin ƙwayar halittu a jami'ar Sao Paulo da ke Brazil ya yi gargadin cewa "hukuncin yana nan" idan aka zo ga batun kimiyya.
"Batun ko soyayya gamon jini ce ko ba gamon jini bace wani abu ne da ake iya ganowa ta ƙwayar halitta wajen samun dacewar abokin zama," a cewarsa.

Asalin hoton, Getty Images
Duk da haka, Ami wanda aka sauya sunansa, yana ganin akwai riba.
Christain, yar shekara 32 wadda ita ma yar Japan ce ta ce tana fatan kulla soyayya ta dacewar kwayar halittta zai taimaka mata wajen samun wanda za su kasance tare.
Tun bayan shiga manhajar kulla soyayya ta Cheiko a shekarar da ta gabata, Ami take soyayya da wasu maza biyu. Ta ce tana fatan za ta yi nasara.
"Lokacin da na hadu da mazan buda biyu, mutane ne masu ilimi sosai kuma ba su da wuyar sha'ani sannan a nutse suke. Amma abin burgewar shi ne duk da cewa suna da kirki, akwai abin da babu amma ban san dalili ba, ban ma san yadda zan yi bayanin lamarin ba.
"Da na yi magana da Cheiko kuma muka duba gwaje-gwajen ƙwayar halittar, duka mazan kamar abokai ne sannan abin da ma ya sa duk da cewa hankalina ya kwanta kasancewa tare da su, babu wani abu na daban. Kuma abin da zai ja hankalina ke nan."
'Yanke shawara cikin hanzari'
Manhajar Cheiko ta ce akasarin mutanen da ke rungumar tsarin dacewar kwayar halitta masu ilimi ne sannan suna aiki a manyan wuraren aiki. Tana ganin saboda duka jinsin biyu ba su da lokacin nemawa kansu aokin zama.
"Ina tunanin mutane za su iya yanke shawara cikin hanzari sannan hankalinsu ya kanta da tsarin amfani da kwayar halitta, wanda shi ne abin da zan iya ba su."
'Yana iya kawo karshen alakar'

Asalin hoton, Alison M jones photography
Melissa, daga Queensland a Australia ta ce tana fuskantar kalubale wajen saurayinta lokacin da ta yanke shawarar yin gwajin dacewar kwayar halitta.
Sun shiga shafin DNA Romance a intanet wanda ya ce yana iya hasashen dacewar soyayya tsakanin mutum biyu ta wasu alamomin ƙwayar halittarsu da ke taka rawa wajen jan hankali".
A baya, Melissa ta ce ta yi samari da dama da basu kasance tare ba, don haka na bata lokaci mai yawa".
A 2017, ta hadu da Mez a manhajar Tinder wanda ya je har Cannes inda suka fara haduwa.
"Na je daukarsa a filin jirgin sama sannan shi ne karon farko da muka hadu," in ji Melissa.
"Gaskiya abin na musamman ne kuma na kasance cikin matukar damuwa, amma ya zo a dai-dai."

Asalin hoton, DNA Romance
Sai dai Melissa ta ce sun fuskanci yan matsaloli a shekarar farko ta soyayyarsu kuma daga baya suka raba gari. Da suka sake dinkewa, ta shawo kan Mez cewa ya kamata su yi gwajin jituwar kwayoyin halitta.
"Bamu fara zama tare ba don haka ina ganin yana da kyau dukanmu mu yi," in ji ta. "Ba wai ya yi murna da hakan ba amma dai ya zo don a yi mana."
Sakamakon gwajin ya nuna an samu jituwar kashi 98 cikin 100 bisa nazarin da aka yi kan kwayar halittarsu".
"A wajena, gani na yi kamar wani karamin tabbaci ne kulluwar alakarmu."

Asalin hoton, Alison M Jones photography
Masanin kimiyyar halittu Rodrigo Barquera daga cibiyar kimiyyar tarihin dan adam Max Planck da ke Jamus ya ce yayin da ake da shaida game da rawar da kwayoyin halittu na HLA ke takawa wajen zabin abokin zama, bai isa ba a yi hasashen nasarar da alakar za ta kasance".
"Waɗannan kwayoyin halittar ba za su damu da komai ba. Ganin cewa alaƙar ɗan adam ta fi rikitarwa fiye da samun yara."
Duk da haka, Melissa ta ce gwajin ya bai wa saurayi da budurwar kwarin gwiwa sannan sun i aure kuma sun kusa haihuwar dansu na farko.
"Ina ganin abin ya yi amma kuma a tunanina ya shafi kimiyya - na yadda da shi. Ba lalle wasu su yadda ba kuma za ma su iya ganin abin banbarakwai."
Ta ce "A wancan lokacin, idan gwajin bai fito yadda ake so ba, to da zai iya zama wani labari ne na daban." "Wataƙila zai iya kawo ƙarshen dangantakar."

Asalin hoton, Melissa
Sienna da Rodrigo Meneses sun ce tsarin kulla soyayya ta gwajin dacewar kwayar halitta da farko kamar ba mai yiwuwa bane a wajen sabbin ma'aurata.
Sai dai wadanda suka
Duk da haka, ma'auratan, waɗanda suka bayyana kansu a matsayin "abokan rayuwa", sun ga dacewar zuwa gwada tsarin don kawai su san yadda tsarin yake. Daga baya aka ce kwayoyin halittunsu sun samu jituwa da kashi 90 cikin 100.
"Abin ya bamu mamaki cewa shafin na iya tabbatarwa a kimiyyance muna son juna amma mun ji dadi matuka sannan mun sake samun kwarin gwiwa kan yadda muke son junanmu."

Asalin hoton, Sienna Meneses
For Dr Meyer, fara amfani da kwayoyin halitta wajen kulla na nuna yadda ake ganin kimiyya.
"Ina ganin wannan yana matukar nuna abubuwan da ake iya yi ta kimiyya."











