Yaƙin yankin Tigray : Yadda wani soja ya tsira bayan shafe awanni 11 ana bata-kashi da bindiga

Asalin hoton, AFP
Wasu sojojin Habasha biyu sun bai wa BBC cikakken labarin yadda dakarun gwamnatin Tigray da a yanzu aka ci su da yaƙi suka kai wa sansaninsu hari da tsakar dare a farkon fara yaƙin a yankin a watan da ya gabata
Dakarun RPLF, wadda ke jagorantar yankin Tigray a baya, sun ce sun kai wani hari ta sama kan sojojin Habasha, yayin da hankalin duniya ya karkata kan zaɓen shugaban Amurka a watan da ya gabata, bayan da suka lura cewa ana ƙoƙarin kai musu hari.
Firaiministan Habasha Abiy Ahmad ya mayar da martani, ta hanyar bayar da umarnin kai harin soji, abin da ya kai ga hamɓarar da gwamnatin yankin, lamarin da ya tilasta wa dakatun na TPL yin ƙundumbalar sakkowa daga tsaunuka domin tunkarar mutanen da suka kira a matsayin ''Masu mamaya''.
Yana da matuƙar wahala samun sahihan bayanai yayin yaƙin saboda katse hanyoyin sadarwa.
Bayanai da jami'an sojin suka yi sun bayana yadda ake samun rarrabuwar kai saboda bambancin ƙabila a rundunar sojin Habasha, da kuma zargin da ake yi wa wasu sojoji da suka fito daga yankin Tigray da goyawa yan uwansu baya.

Sajan Bulcha:
Ina wani sansanin soja dake kusa da birnin Adigrat, da ke iyaka da Eritriya. Kusan karfe 11:30 na ranar 3 ga watan Nuwamba, muka samu sakon kar ta kwana daga wajen yan uwanmu, da ke kauyen Agula, mai nisan kilomita 30 daga babban birnin Tigray wato Mekelle, inda a saƙon suka bayyana mana cewa "An kewaye mu, idan kuna da halin zuwa ku taimaka mana, ku taho".
Ba da jimawa ba, mu ma sai aka kewaye namu sansanin. Ɗaruruwan dakarun Tigray ne da sauran mayaƙa ɗauke da makamai a tsaitsaye, cikinsu har da wasu wasu sojojinmu da suka bar sansani, a lokacin sai suka koma suka haɗe da su.
A lokacin ne muka je ga Kanal ɗinmu wanda yake riƙe da mukullin wurin da makamanmu ke ajiye muka ce ya buɗe mana.

Asalin hoton, AFP
Sai ya ƙi ya buɗe mana, a kan cewa ba a ba shi umarnin yin hakan ba. Dan Tigray ne, don haka sai muka yi tunanin da shi aka shirya hakan.
Wasu daga cikin sojojinmu sai suka har cacar baki da shi, daga ƙarshe dai muka ɓalle wajen muka ɗebi makamanmu a lokacin tuni mayakan TPLF suka fara buɗe wuta.
Sai muka ja daga a ciki da wajen sansaninmu, muka riƙa amfani da manyan duwatsu da duro-duro da bango don kare kai daga harbin harsashi, wajajen ƙarfe 1 na rana.
Akwai nisan akalla mita 50 tsakaninmu da su.
Mun kashe sama da mayaƙansu 100, su kuma suka kashe mana namu 32. a iya tamu tawagar an kashe mana soja ɗaya tare da raunata guda tara.
Yawanci sojojinmu da suka koma ɓangarensu ne suka kashe mana mutanenmu.
An shafe kusan awa 11 ana bata-kashi har zuwa faɗuwar rana, inda da misalin ƙarfe 4 na yamma suka nemi a tsagaita wuta, aka nemi me ba su dukkanin kayanmu na soji muka amince muka yi hakan.
'Na bada sunan ƙarya'
A lokacin ne mayaƙan na su suka kai mu wani sansaninsu da ke kauyen Abiy Adidi, a garin Adigrat.

Babu wanda ya duba lafiyar sojojinmu da aka raunata mana a lokacin.
Duk safiya ana kiranmu daya bayan ɗaya, inda ake bukatar mu fadi sunayenmu, kabilarmu da kuma matsayinmu a soja, kullum sai in musu ƙarya idan sun tambaye ni.
Wajen kamar yankin sahara, domin yana da tsananin zafi
Sun bamu ruwa kadan, sannan da safiyar kowacce rana aka ba mu shayi mara suga a wata robar ruwa da aka yanke samanta, sannan abincin ma da suke ba mu wani motsattsen biredi ne dan mitsitsi.
'An bankawa kakinmu wuta'
Bayan shafe kusan mako biyu, sai suka ba mu zabi uku, ko dai mu hade da su, ko mu ci gaba da rayuwa a Tigray, ko mu koma gidajenmu, sai muka dauki zabi na karshe.
Amma ba a bai wa manyan kwamandojinmu da mata wannan zabi ba, sai aka ci gaba da rike dubbansu a kauyen Abiy Adidi.

Asalin hoton, Getty Images
Da misalin karfe 15:00 na ranar Juma'a ne aka sa mu duka mu hau manyan motoci. Bugu da ƙari, mun ɗauki yan uwanmu da suka samu raunuka.
Mun zauna cikin manyan motocin daukar kaya a cunkushe har muka bar Abiy Addi da misalin karfe 23:00.
Mun yi tafiyar tsawon awanni a kan titunan baya har sai da sojojin na musamman na TPLF - wadanda ke rakiyar motocinmu - suka sa mu a bakin Kogin Tekeze da ke kan iyakar tsakanin Tigray da makwabtan jihar Amhara.
Motocin sun zo a lokuta daban-daban. Dukanmu mun shiga kwale-kwale sai da aka shafe kimanin awanni shida muna tafiya.
Daga nan muka yi tafiyar kimanin awanni 16 domin isa garin Sekota a cikin Amhara.
Yanzu haka muna cikin harabar ofishin yan sanda a garin.
Ana ciyar da mu sosai kuma ana kula da mu da kyau. Ana kula da wadanda suka jikkata a asibiti, fiye da makonni uku bayan harin.
Na ji wasu daga cikinsu sun mutu a hanya, kuma an bar gawarwakinsu.

Kopral Ibrahim Hassan:
Na shafe kusan shekara takwas ina aikin soja. Ni ma ina Adigrat, amma a wani sansanin. Ni ne mai gadin da ke bakin aiki a ranar 3 ga Nuwamba, ina gadi ne daga karfe 22:00 zuwa tsakar dare. Wasu daga cikin sojojin tuni suna bacci.
Kai tsaye bayan na gama aiki sai na ji karar harbe-harbe. Ban san abin da ke faruwa ba. Na je na gani.
Sai na tarar tuni sojoji na musamman da dakaru na musamman na TPLF sun kewaye sansaninmu, kuma suka shiga ciki. Yawancinmu ba mu da makamai.

Asalin hoton, Getty Images
Sai suka umarci sojoji, har da ni, da mu mika wuya. Ba mu yarda ba, muna cewa sojojin tarayya ba za su iya mika wuya ga sojojin yankin ba. Amma a ƙarshe mun yarda da umarnin manyanmu, waɗanda 'yan Tigrayan ne.
Mun kasance a cikin sansanin har zuwa 6 Nuwamba. Daga nan sai sojojin TPLF suka yi jigilar mu da manyan motoci zuwa wani karamin gari, Idaga Hamus, kusan kilomita 26 daga inda muke. An ajiye mu a can har tsawon sati sannan aka kai mu wajen Abiy Addi.
A can, mun sami mutane da yawa masu biyayya ga gwamnatin tarayya, daga 'yan sanda, da sojoji da sojojin sama.
Mun kasu kashi biyu, kuma an ajiye mu a wurare daban-daban guda uku - sansanin soja, da makarantar horo da kuma wani fili.
Babu ruwan wanka, ruwan sha ma dan kadan ne. Kamar dai an bar mu mu mutu a cikin wannan hali.
Mun kwana a ƙananan ɗakuna a cikin mawuyacin yanayi.
Bayan da muka shafe kusan mako uku ne sai aka bamu zabi, idan muna da aure tare da yara a Tigray, za mu iya rayuwa a matsayin farar hula, ko mu shiga cikinsu, ko mu bar garin.
Sai dai wadanda suka iya amfani da manyan makamai da manyan kwamandoji sun tsaya a baya.











