Abin da rikici a yankin Tigray na Ethiopia yake nufi

Asalin hoton, AFP
Rikici tsakanin dakarun gwamnatin tarayya na Ethiopia da kuma na yankin Tigray ya jefa yankin cikin hali na rashin zaman lafiya.
An shafe kusan mako biyu ana rikici, wanda ya dagula al'amura a ƙasar da ta fi kowace yawan mutane a yankin Gabashin Afrika.
Rikicin siyasa da na neman mulki da kuma neman kawo sauyi a siyasar ƙasar na daga cikin abubuwa da dama da suka yi sanadiyyar rikicin.
A wannan maƙalar, an yi bayani kan dalilin da ya sa rikicin da ƙara ƙaruwa da kuma abin da hakan ke nufi ga makomar ƙasar.

Asalin hoton, Reuters
An fara rikicin ne a ranar 4 ga watan Nuwamba, a lokacin da Firaiministan Ethiopia Abiy Ahmed ya bayar da umarnin ƙaddamar da yaƙi kan dakarun yankin Tigray.
Ya ce ya bayar da wannan umarnin ne domin mayar da martani kan wani hari da aka kai wani sansanin soji da ke ɗauke da sojojin tarayyar ƙasar a yankin Tigray.
Ƙara ruruwar rikicin ta samo asali ne sakamakon rashin jituwar da ke tsakanin gwamnatin Mista Abiy da kuma jagororin Jam'iyya mafi ƙarfi a yankin na Tigray.
Sama da shekara 30, jam'iyyar ce ke gudanar da gwamnati, amma bayan zuwan Mista Abiy kan mulki, ya jingine ta gefe guda.
Mista Abiy dai ya hau mulki ne a 2018 bayan an sha fama da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati.
Mista Abiy ya yi ta bibiyar a kawo sauyi na tsare-tsare, sai dai ko da yankin Tigray ya ƙi amincewa da hakan, sai aka samu rikici.
Musabbabin rikicin Yankin Tigray da Gwamnatin Ethiopia
Wannan rikici ya samo asali ne daga tsarin gudanar da gwamnatin ƙasar Ethiopia.
Tun a 1994, Ethiopia na amfani da tsari irin na Federaliya wanda hakan ya sa ƙabilu da dama ke lura da gudanarwar yankuna 10 na ƙasar.
Idan aka tuna, wannan jam'iyyar dai mai ƙarfi ta yankin Tigray - Tigray People's Liberation Front (TPLF) - ta taka muhimmiyar rawa wurin samar da wannan tsari.
Jam'iyyu huɗu ne suka yi haɗaka suka samar da shugaba da ya mulki ƙasar tun daga 1991, bayan an yi wa sojoji juyin mulki.
Sakamakon haɗakar da aka yi, hakan ya sa Ethiopia ta zama ƙasa wadda ta rinƙa samun ci gaba da zaman lafiya, sai dai an ta samun ƙorafi kan batun take haƙƙin bil adama da kuma yanayin dimokraɗiyya a ƙasar.
Rashin gamsuwar 'yan ƙasar ya jawo zanga-zanga, wanda hakan ya jawo aka yi garambawul ga gwamnatin ƙasar, har Mista Abiy ya zama Firaiminista.
Mista Abiy, ya samar da 'yancin siyasa ta hanyar kafa sabuwar jam'iyya (the Prosperity Party), inda kuma ya cire manyan 'yan yankin Tigray daga muƙaminsu bayan zarginsu da cin hanci da rashawa.
Haka kuma, Mista Abiy ya kawo ƙarshen rikicin yanki da aka daɗe ana yi tsakanin ƙasar da Eritrea, wanda hakan ya sa ya samu kyautar Nobel ta zaman lafiya a 2019.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan kyautar da Mista Abiy ya samu ta jawo ya yi fice, amma kuma hakan ya jawo masa caccaka daga yankin Tigray.
Jagororin Tigray na kallon tsare-tsaren Mista Abiy a matsayin wata hanya ta lalata tsarin Fediraliya a ƙasar inda suke ganin gwamnatin tarayya za ta ƙwace ƙarfin ikon ƙasar.
Rikici tsakanin bangarorin biyu ya ƙara tsami bayan da yankin na Tigray ya yi watsi da umarnin gwamnatin tarayya ya yi gaban kansa ya gudanar da zaɓe a yankin. A baya dai gwamnatin tarayyar ƙasar ta dakatar da zaɓen ne saboda annobar korona.
Sai kuma a watan Oktoba, rikicin ya ƙara ɗaukar zafi bayan da gwamnatin tarayyar ƙasar ta dakatar da bayar da kuɗi da yanke hulɗa da yankin na Tigray. Gwamnatin gudanarwa a yankin na Tigray sai ta ce hakan kamar "jawo yaƙi" ne a ƙasar.
Tun daga nan fargaba sai ta ƙaru, inda Mista Abiy ya ce Tigray sun wuce gona da iri.
Ya zargi dakarun Tigray da kai hari a sansanin soji na tarayyar ƙasar tare da satar makamai.
Ethiopia, wadda ita ce ƙasar Afrika da ta fi kowace daɗewa a matsayin ƙasa mai 'yancin kanta, an samu sauye-sauye a ƙasar matuƙa tun bayan da Mista Abiy ya hau kan karagar mulki.
Mista Abiy, wanda ɗan ƙabilar Oromo ne, ƙabilar da ta fi kowace girma a ƙasar, ya buƙaci da a kawo sauyi kan siyasar ƙasar, da kuma samar da haɗin kai da a jawabinsa na farko a matsayin Firaiminista.

Asalin hoton, Getty Images
'Yan siyasa daga yankin na Tigray da suka jagoranci ƙasar na shekara 27, ana kyautata zaton suna daga cikin waɗanda suka jawo matsala.
A shekarun 1970 da 1980, jam'iyyarsu ta TPLF ta yi yaƙi domin ta ƙwace iko daga gwamnatin sojoji. Jam'iyyar ta samu nasara, inda ta zama jagorar haɗakar waɗanda suka karɓi mulki a 1991.
Haɗakar gwamnatin ta bayar da ƙarfin iko ga yankunan Ethiopia, amma duk da haka aka bayar da ƙarfin gaske ga tarayyar ƙasar, inda wasu ke caccaka da cewa gwamnatin tarayyar na danne 'yan adawa.

A yanzu dai wannan jam'iyya ta koma jam'iyyar adawa a ƙasar.
A 2019, jam'iyyar ta ƙi yarda ta haɗe da sabuwar gwamnatin Mista Abiy da kuma jam'iyyarsa ta Prosperity Party.

Asalin hoton, Getty Images











