Yankin Tigray: Yaƙin Habasha na dab da ƙarewa in ji firaminista Abiy
Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya ce ayyukan sojin da ake yi a yankin arewacin Tigray ya shiga matakin ƙarshe a yanzu da wa'adin kwana uku da aka bai wa mayaƙan don su miƙa wuya ya ƙare.
A ƙalla rikicin ya sa mutum 27,000 sun tsere zuwa maƙwabciyar ƙasar Sudan.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutane za su shiga wani mummunan yanayi.
Rikicin ya fara ne kusan mako biyu da suka gabata a yayin da tashe-tashen hankula tsakanin gwamnatocin gwamnatin tarayya da na yanki suka yi ƙamari.
Faɗa ya barke bayan da gwamnatin Habasha ta zargi ƙungiyar da ke fafutikar ƴantar da al'ummar Tigray ta TPLF, wacce ke iko da yanki Tigray, da cin amanar ƙasa da kuma mamaye sansanin sojoji.
Ƙungiyar TPLF na ganin gwamnatin tarayyar ƙasar a matsayin wacce ba halastacciya ba.
Majalisar Ɗinkin Duniya na fargabar yawan masu tsere wa daga Habasha ƙalilan ne kawai daga cikin ɗumbin mutanen da yaƙin ya tilasta wa barin gidajensu, sannan zuwa yanzu hukumomin agajin ba sa iya samun damar shiga yankin Tigray.
Rikicin ya kuma yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mutane, amma samun bayanai daga Tigray na da wahala saboda an toshe hanyoyin sadarwa.

Asalin hoton, AFP
Gwamnatocin yankin gabashin Afirka da suka haɗa da Uganda da Kenya sun yi kira da a sasanta don cimma mafitar zaman lafiya kan rikicin.
Gwamnatin Habasha ta cire batun tattaunawa da ƙungiyar TPLF.
Me kuma Firaminista Abiy ya ce?
A wani saƙon da ya wallafa a Facebook, Firaministan ya gode wa mayaƙan TPLF waɗanda ya ce sun yi amfani da damar wa'adin kwana uku sun miƙa wuya amma bai faɗi yawansu ba.
Ya ce gwamnatinsa a shirye take ta karɓi tare da sadar da ƴan uwanmu ƴan Habasha da danginsu waɗanda suka tsere zuwa maƙwabtan ƙasashe.
Yaya girman matsalar da mutane ke ciki?
Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNHCR ta ce mutane na fuskantar shiga cikin mummunan yanayi kuma dubbai sun tsere saboda yaƙin.
Hukumar a shirye take wajen bayar da taimako a Tigra a duk lokacin da hanya ta samu kuma idan akwai tsaro, a cewar mai magana da yawunta Babar Baloch.
''Akwai mutane da dama da suka rabu da muhammancinsu a cikin Tigray kuma lallai hakan abin damuwa ne, sannan muna ƙoƙarin shirya abin da ya dace,'' in ji Jens Laerke, wani mai magana da yawun ofishin hukumar jin ƙai.
Yaya munin rikicin?

Ɗaruruwan mutane ne rahotanni suka ce sun mutu a Habasha tun farkon ɓarkewar rikicin ranar 4 ga watan Nuwamba.
Ƙungiyar kare haƙƙn ɗan adam ta Amnesty International ta ce ta tabbatar da mutuwar ɗaruruwan mutanen da aka kashe ta hanyar caka musu wuƙa a garin Mai-Kadra (May Cadera) a ranar Litinin ɗin makon jiya.
Firaminista Abiy ya zargi dakarun da ke goyon bayan shugabannin Tigray da yin kisan kyashi. TPLF ta ƙaryata cewa taba da hannu sannan tana maraba da bincike mai zaman kansa na ƙasa da ƙsa.
Hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta Habasha ta ce za ta tura tawaga don yin bincike.
Me ya sa gwamnati ke da TPLF ke faɗa?
TPLF sun mamaye rundunar soji da kuma ɓangaren siyasar ƙasar tsawon shekaru kafin Mista Abiy ya karɓi mulkin a shekarar 2018, kuma sun aiwatar da manyan sauye-sauye.
A bara, Mista Abiy ya rushe gamayyar da ke mulkin, wacce ta haɗa da jam'iyyun yankuna da na ƙabilu daban-daban ya mayar da su jam'iyya ɗaya tilo ta ƙasar, wacce TPLF suka ƙi shiga ciki.

Rikicin ya sake ta'azzara a watan Satumba, lokacin da aka y zaɓen yanki a Tigray, ta hanyar yin watsi da umarnin cewa kar a yi kowanne irin zaɓe saboda annobar cutar korona. Mista Abiy ya mayar da martani ta hanyar kiran zaɓen wanda bai halasta ba.
Hukumomin yankin Tigray na kallon sauye-sauyen Mista Abiy a matsayin ƙoƙarin miƙa wa gwamnatinsa ta tarayya ƙarin ƙarfin iko da raunana gwamnatocin jihohi,

Mr Abiy ya samu kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 2019 saboda ƙoƙarinsa na kawo zaman lafiya tsakanin ƙasar da Eritrea.
Firaministan ya yi amannar jami'an TPLF na raina ƙarfin ikonsa.
Mr Abiy ya bai wa sojoji umarnin dirar wa mayaƙan TPLF bayan da ya ce sun wuce gona da iyaka.
Ya zarge su da kai hari kan sansanin sojin inda dakarun gwamnatin tarayya suke a ranar 4 ga watan Nuwamba, yana mai kiran lamarin da cin amanar ƙasar. Sai dai TPLF sun yi watsi da batun cewa sun kai hari sansanin.












