Yankin Tigray: Abu huɗu da kuke buƙatar sani kan rikicin ƙasar Habasha

Bayanan bidiyo, Bidiyon abu huɗu da kuke buƙatar sani kan rikicin ƙasar Habasha

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Tashe-tashen hankula na ci gaba da ruruwa tsakanin yankin Tigray da hukumomin gwamnatin tarayyar Habasha a babban birnin ƙasar Addis Ababa.

Firaminista Abiy Ahmed, ya zargi dakarun da ke goyon bayan gwamnatin yankin Tigray ta The People's Liberation Front (TPLF), da kai hari kan sansanin sojin tarayya ya kuma tura sojojin Habasha.

Ƙaruwar tashe-tashen hankulan ya jawo yaɗuwar rikicin cikin gida zuwa kan iyakokin.