Rikicin Tigray : 'An yiwa farar hula kisan gilla, in ji Amnesty

Sojoji dauke da bindiga a cikin mota

Asalin hoton, Reuters

Daruruwan farar hula aka yi wa 'kisan gilla' a rikicin yankin Tigray na arewacin Habasha, in ji ƙungiyar kare haƙƙin dan adam ta Amnesty.

Shaidu sun dora alhaki kan dakarun da ke biyayya ga ƙungiyar fafutikar 'ƴantar da al'ummar Tigray ta TPLF kan kisan na ranar Litinin, sai dai jami'an Tigray sun yi watsi da cewa akwai hannun dakarun da ke musu biyayya.

Fada tsakanin dakarun gwamnatin da na yankin Tigray ya soma ne a makon da ya gabata.

Ana fuskantar matsaloli wajen samun bayanai, ba bu layukan wayoyi sannan an katse intanet.

Bayanan bidiyo, Bidiyon abu huɗu da kuke buƙatar sani kan rikicin ƙasar Habasha

Wannan na iya kasancewa adadi mafi yawa na farar hula da aka kashe a rikicin.

Akwai ɗaɗadɗiyar tsama a dangantakar tsakanin gwamnatin Habasha da ƙungiyar TPLF, da ke iko da Tigray, yanayi ya kai ga rikici tsakanin sojoji, da hare-haren sama da dakarun gwamnati suka rinka kai wa yankin.

Sakamakon haka, dubban farar hula suka tsere daga yankin zuwa Sudan, da tace za ta basu matsugunai a sansanin gudun hijira.

Me Amnesty ta ce?

A wata sanarwar da ta fitar Amnesty ta ce akwai tabbacin "kashe gwamman in ba daruruwa ba, an caccaka wa mutane wuka da kisa ta azabtacciyar hanya a Mai-Kadra wani gari a kudu maso yammacin yankin Tigray na Habasha a daren 9 ga watan Nuwamba".

Akwai hotunan gawawwaki da bidiyon da aka naɗa wasu kan tituna wasu kuma ana tura su kan gadon marassa lafiya."

Bayanan bidiyo, Bidiyon abu huɗu da kuke buƙatar sani kan rikicin ƙasar Habasha

Amnesty ta ce akasarin wadanda aka kashe masu fita aikin leburanci ne da babu ruwansu da rikicin.

Daraktan Amnesty a gabashi da kudancin Afirka, Deprose Muchena, ya bayyana yanayin da "tsantsan mugunta" tare da bukatar gwamnati ta dawo da sadarwa da ba da damar sa ido kan abubuwan da ke faruwa.

Amnesty ta ce shaidu sun bayyana irin "baƙar azaba da raunukan da aka ji musu ta hanyar amfani da makamai irinsu wuka da adsa". Wasu shaidu sun ce maharan da ke far musu dakaru ne da ke biyaya ga ƙungiyar TPLF wadanda sojojin gwamnati suka murkushe a wani yanki mai suna Lugdi.

Map
1px transparent line

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana fuskantar barazana wajen iya kai kayan agaji ga dubban mutanen da ke cikin haɗari sakamakon rikicin.

Mene ne asalin rikicin?

A ranar 4 ga watan Nuwamba Firaminista Abiy Ahmed ya umarci dakarun gwamnati su kai hari kan dakarun Tigray bayan ya ambata cewa an kai wa sansanonin soji hari.

An samu rikici sosai da hare-haren sama tun daga lokacin.

A ranar Alhamis Mr Abiy ya ce dakarun gwamnati na samun gagarumar nasara a yankin.

Ƙungiyar TPLF ta kasance mafi karfin mambobi a gamayyar jam'iyyun da ke mulkin Habasha a tsawon shekaru sai dai Mr Abiy ya dakile tasirinta bayan hawa mulki a 2018 kuma TPLF ta bijirewa shiga jam'iyyar da aka hade wuri guda.

Shugabanin Tigray sun ce ana musu rashin adalci da zarge-zagen rashawa.

Mr Abiy ya zargi wasu daga cikin shugabanin Tigray da "rashin adalci" da adawa da shirin sa na sake fasalta Habasha.