Buhari ya cire Kachikwu daga shugaban NNPC

Shugaban Najeiya Muhammadu Buhari, ya sauke manajan darakta na kamfanin man fetur na kasar NNPC, Ibe Kachikwu, a ranar Litinin.
Shugaban ya kuma amince da nadin hukumar gudanarwa ta NNPC, kamar yadda aka tanada a dokar kamfanin NNPC ta shekarar 1997.
Sai dai kuma, shugaba Buhari ya bar Mista Kachikwu a matsayinsa na ministan man fetur na kasar kuma shugaban rukunin daraktoci na NNPC.
Sabon manajan daraktan kamfanin man fetur din dai shi ne Maikanti Kacalla Baru.






