An kashe kwamandan Hezbollah

Akwai dubban mayakan Hezbollah a Syria.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto, Akwai dubban mayakan Hezbollah a Syria.

Kungiyar mayakan Hezbollah ta sanar da rasuwar babban kwamandanta, Mustapha Amine Badreddine, a birnin Damascus na Syria.

Hezbollah ta ce Mustapha ya rasu ne sakamakon wani tashin bam kusa da filin jirgin saman birnin, wanda ake zargin Isra'ila ta kai.

Daman dai ana tuhumar Bedreddine da kitsa kisan da aka yi wa tsohon firaiministan Lebanon, Rafik Hariri, a Beirut, a 2005.

Ita dai Hezbollah ta kasance tana marawa shugaban Syria, Bashir al-Assad baya, a inda ta aike da dubban mayakanta zuwa kasar.