Za a wallafa sunayen masu fyade a India

Asalin hoton, AP
Gwamnatin India ta ce tana shirye-shiryen wallafa sunayen duk mutanen da aka samu da laifin yi wa mata fyade.
Gwamnatin ta ce za a wallafa sunayen ne, da suka hada da adireshi da hotunan mutanen.
Ta kara da cewa mutanen da za a wallafa sunayensu za su hada da wadanda shekarunsu ba su kai 18 ba.
Jami'ai a kasar sun ce za a ji ra'ayoyin mutane kan wannan batu.
An dauki matakin ne bayan wani gungun masu aikata laifuka ya yi wa wata yarinya fyade, sanna ya kashe ta a birnin Delhi, fiye da shekara uku da suka wuce.
Lamarin dai ya yi matukar harzuka jama'a.






