Kai tsaye: Mata 100, rabin al'ummar duniya
<link type="page"><caption> Latsa nan domin sabunta shafin:</caption><url href="http://www.bbc.com/hausa/news/2015/12/151201_live_page_100women_hausa.shtml" platform="highweb"/></link>

A ci gaba da shirinmu na "mata 100, rabin al'umar duniya", yau za mu kawo muku muhawara kai tsaye kan kalubalen da mata ke fuskanta.
Mun kammala kawo muku bayanai kai-tsaye game da "Mata 100, Rabin Muryar Al'umar Duniya". Da fatan kun ji dadin kasancewa tare da mu. Mun gode

3:19 Ka da ku manta, muna gabatar muku da bayanai ne kai-tsaye game da muhawara kan "Mata 100, Rabin Muryar Al'umar Duniya".


2:47 Ziya'atulhaq Usman ta ce bai kamata a rika barin mata suna shugabanci ba saboda, a ganinta, tunda Alkur'ani bai amince su yi shugabanci ba, ya kamata su guji nemansa.

2:23 Mata na ci gaba da yin tsokaci kan kalubalen da suke fuskanta da hanyoyin da za su shawo kansu.

12:58 Hauwa Mohammed ta ce ya kamata mata su rika yi wa maza biyayya, amma bai kamata maza su hana mata neman na-kai ba.
12:35 Bara'atu Aliyu ta ce ba sai mace tana da kyau ba za ta taka rawa wajen ci gaban dan adam. Ta bayar da misalan mata da dama da ta ce ba kyawawa ba ne, amma suna yin zarra a fannonin rayuwa daban-daban.


11:56 Mun kammala zagayen farko na muhawarar da muke yi kan kalubalen da mata ke fuskanta.

11:28 Shin ya kamata mata su zama boyi boyin maza?

11:15 Lydia Samson ta ce ba sai mace tana da kyau ba za ta iya yin zarra a wurin aikinta.
10:55 Rafat Salami ta gidan rediyon Voice of Nigeria ta ce akwai gagarumar rawar da mata za su taka wajen inganta rayuwar al'umma.

10:20 Wasu alkaluma sun nuna cewa maza sun fi mata yawa a harkokin watsa labarai. Ta yaya za a cike wannan gibi?

09:43 Za mu gudanar da muhawarar ce da rukunai hudu na mata, kuma za mu fara da mata 'yan jarida.










