"Rashin Saddam da Gaddafi masifa ce"

 Donald Trump ya zargi Obama da raba kawunan Amurkawa.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto, Donald Trump ya zargi Obama da raba kawunan Amurkawa.

Mutumin da ke son tsayawa takarar shugabancin Amurka, Donald Trump, ya ce duniya sai tafi samun zaman lafiya da tsofaffin shugabannin Iraki da Libya Saddam Hussein da Muammar Gadaffi suna ci gaba da mulki.

Mr Trump ya bayyana yankin Gabas ta Tsakiya a matsayin mai cike da "bala'i", wanda al'amura suka kara dagulewa karkashin kulawar Shugaba Obama da Hillary Clinton.

Mr Trump ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan talabiji na CNN.

Ya kara da cewa manufofinsa na kasashen waje za su mayar da hankali ne wajen karfafa aikace-aikacen sojojin Amurka.

Ya zargi Shugaba Obama da raba kawunan Amurkawa, yana mai cewa idan ya ci zabe zai hada kan 'yan kasar.