Kwayar Ebola kan dade a jikin mutum

Asalin hoton, SCIENCE PHOTO LIBRARY
Wani sabon bincike ya gano cewa kwayar cutar Ebola kan iya dadewa a cikin jikin namiji da ke dauke da ita har tsawon watanni tara fiye da yadda aka yi tsammani.
Masu binciken sun yin nazarin a kan maniyin wasu maza su kusan 100 daga kasar Saliyo wadda ta farfado daga cutar ta Ebola.
Kashi daya bisa uku daga ciki suna dauke da kwayar cutar ta Ebola, kuma bayan watanni bakwai zuwa tara suka soma rashin lafiya.
Sai dai babu cikakken bayani a kan ko za su iya baza cutar.







