Shan barasa yana kawo cutar daji

Masana kimiyya sun ce shan barasa ko da sau daya ne ko biyu kuma ko mutum bai yi mankas ba, yana jawo cutar daji wato cancer.
Wani nazari da aka wallafa a mujallar lafiya ta British Medical Journal, ya yi duba ga manyan bincike biyu da aka gudanar a Amurka, wadanda aka yi a kan fiye da mutane 100,000.
Binciken ya gano cewa an fi kamuwa da dajin mama.
Masana sun ce sakamakon binciken ya jaddada binciken da aka yi a baya wanda ke bukatar mutane su rage yawan shan barasa.
Sun kuma jero hadurran da ke tattare da shan barasar kamar haka:
■Barasa na da alaka da karuwar hadarin kamuwa da cutar dajin baki ko makogwaro ko hanji ko hanta ko kuma dajin mama.
■Shan sigari da shan barasa a lokaci guda na kara hadarin kamauwa da cutar dajin.
■Dukkan barasa kowacce iri ce na jawo cutar daji.
■Yawan shan barasar da mutum ke yi tamkar yana kara kusantar cutar ne.
■Bari shan barasa kuwa na rage hadarin kamuwa da cutar dajin.
Cutar daji dai na daya daga cikin cututtukan da suka addabi al'umma a wannan zamani, kuma har yanzu magance ta na da matukar wahala.










