NDLEA ta kama daloli a Lagos

Asalin hoton, AFP
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya, NDLEA ta kama wani mutum dauke da sama da $2m a filin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke a Lagos.
Wanda aka kama ya bayyanawa hukumar cewa zai kai kudaden ne Abuja domin a canza su.
Sai dai NDLEA ta ce an samu kudaden ne ta hanyar safarar hodar Iblis.
Hukumar ta ce mutumin ya bayyana mata cewa shi dan-canji ne.
'Yan Najeriya dai na fita da kudaden da ake zargin sun sata zuwa kasashen waje abin da ya sa aka tsananta bincike a kan iyakokin kasar.







