Soji sun kwashe 'yan gudun hijira daga Adamawa

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce sojojin kasar sun kwashe mata da yara kusan 300 daga sansanin 'yan gudun hijira da ke jihar Adamawa.
Rahotanni sun ce an yi amfani da jirgin saman soji wajen kwashe matan daga sansanin a Malakoyi.
Jami'in hukumar NEMA mai kula da shiyyar arewa maso gabas Alhaji Kanar Muhammad, ya shaida wa BBC cewa an kwashe mutanen ne saboda a basu kulawa ta musamman, sai dai ya musanta zargin cewa wasunsu na da alaka da kungiyar Boko Harama.
Kawo yanzu dai hukumomin sojin Najeriya ba su bayyana inda aka kai mutanen ba.
A watan Afrilun da ya gabata ne dai sojojin suka ceto mutanen daga dajin Sambisa a yakin da suke yi da 'yan kungiyar Boko Haram.






