Bamu ga iyayen yara 192 ba - NEMA

Asalin hoton, AFP
Hukumar NEMA ta ce yara 'yan gudun hijirar da ba a san inda iyayensu ko danginsu suke ba, sun kai 192 a sansanonin da ke jihar Adamawa.
Jami'in hukumar na Arewa-maso-gabashin kasar, Muhammad Kanar, ya shaida wa BBC cewa hare-haren kungiyar Boko Haram a yankin ne ya daidaita yaran da suka samu kansu a sansanoni biyar na jihar.
Inda ya kara da cewa "A yanzu haka kalilan daga cikin yaran na tare ne da iyalan makwabtan da suka sani a da, yayin da ragowar da basu san kowa ba ke karkashin kulawar jami'an NEMA na musamman."
Jami'in ya ce yaran na zuwa makaranta a cikin sansanonin na 'yan gudun hijira.
Daruruwan yara ne dai suka samu kansu ba iyaye ko dangi sakamakon kashe iyayen ko tserewar da suka yi a hare-haren da Boko Haram ke kaiwa a arewa-maso-gabashin kasar.
Hukumar NEMA ta ce mutane fiye da miliyan daya ne suka rasa muhallansu sakamakon rikicin Boko Haram a cikin shekaru biyar da suka wuce.






