Ebola: Mace daya ta rage a asibiti

Asalin hoton, Reuters
Hukumomin lafiya a Nigeria sun ce mata daya ce tak ta rage ake yi wa magani daga cikin wadanda suka kamu da cutar Ebola a kasar.
A cewarsu, ana sa ran sallamarta daga asibiti a cikin wannan mako saboda babu sauran alamun cutar Ebolan a jikinta.
A taron manema labarai a Abuja, Ministan lafiya na kasar, Farfesa Onyebuchi Chukwu ya ce mutane 11 daga cikin 19 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar, sun warke, yayin da 7 suka mutu.
Kwanaki hamsin kenan cif da bullar cutar Ebola a Nigeria bayan da wani dan kasar Liberia, Patrick Sawyer ya shigo da cutar cikin kasar.
Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce cutar Ebola ta hallaka mutane fiye da 2,000 a wasu kasashen yammacin Afrika.







