Amurka za ta tunkari yaki da IS

Asalin hoton, na
Shugaban Amurka Barack Obama ya ce a ranar laraba mai zuwa zai baiyana shirin sa na tunkarar kungiyar kasar musulunci.
A cikin wata hira ta gidan talabijin din Amurka Mr Obama yace zai kassara karfin kungiyar da dakile yankunan da ta mamaye da kuma murkushe su.
Sai dai ya fayyace cewa shirin na sa bai kunshi shigar sojoji ta kasa ba.
Yace wannan ba kwatankwacin yakin Iraqi ba ne yaki ne da ta'addanci wanda da ma Amurkar ke yi akai akai a tsawon shekaru biyar zuwa bakwai.







